Home / Lafiya / Masari Ya Bude Katafaren Ginin Ma’aikatan Kiwon Lafiya A Katsina

Masari Ya Bude Katafaren Ginin Ma’aikatan Kiwon Lafiya A Katsina

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana sabon tsarin tara kudin fansho tsakanin Gwamnati da ma’aikata a matsayin tsayayyen tsarin da kowa zai amfana bayan ajiye aikinsa.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen babban taron bude katafaren ginin da kungiyar ma’aikatan lafiya reshen Jihar katsina suka gina a cikin birnin Katsina.

 

Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa, da yardar Allah, Gwamnatin shi ba za ta bar ma wadda za ta gaje bashin kudaden aje aikin ma’aikata ba.

Gwamnan ya bada wannan tabbaci ne wajen bukin bude wani masabkin baki da kuma rukunin shaguna da kungiyar ma’aikatan lafiya reshen jihar Katsina ta gina a kan titin Goruba dake nan cikin birnin Katsina.

Alhaji Aminu Masari ya bayyana cewa a duk wata, gwamnati na kashe sama da Naira Miliyan Dubu Daya da Dari biyu (N1.2B) wajen biyan kudin fansho duk wata, kuma a kullum wannan kudi karuwa suke saboda karuwar masu aje aiki, ya kara da cewa yanzu haka shugaban ma’aikata na jiha ya turo mashi da takardar aje aiki (ritaya) ta Daraktoci guda ashirin (20) daga Ma’aikatar Ilimi ta jiha.

“Gwamna Masari ya ankarar da shugabannin kwadago da ma’aikata cewa sabon tsarin tara kudin fansho na hada ka tsakanin gwamnati da Ma’aikata shi ne tsayayyen tsarin da zai kawar da duk wata barazana wajen biyan hakkokin wadanda suke aje aiki kan lokaci”.

Ya kuma yaba wa shuwagabannin kungiyar ma’aikatan lafiyar a kan yadda suke sanya ya kamata wajen kashe kudaden da ma’aikatan suke tarawa.

A karshe ya kuma yi kira ga al’umma baki daya da kada mu gajiya wajen addu’o’in Allah Ya kawo mana dauki kan matsalolin da jiha da kasar ke ta fuskanta musamman na wannan lokacin.

 

Babban taron dai ya samu halartar yayan kungiyar daga ko’ina domin nuna farin ciki da goyon bayan kungiyar.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.