Home / Big News / Masari Ya Kafa Dokar Hana Fita A Birnin Katsina

Masari Ya Kafa Dokar Hana Fita A Birnin Katsina

Imrana Abdullahi
Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya bayyana kafa dokar hana fita a cikin birnin Katsina biyo bayan samun wadansu mutane biyu da cutar Covid – 19 da ake kira Korona bairus dokar dai za ta fara aiki ne daga karfe Bakwai na ranar Talata mai zuwa.
Da yake yi wa manema labarai bayani a gidan Gwamnati na  Katsina, Gwamna Masari ya shaida masu cewa yawan Mutanen da aka samu a halin yanzu suna dauke da Cutar Covid – 19 a Jihar sun kai Goma sha biyu (12).
Ya ci gaba da shaidawa manema labarai cewa Gwamnati nan bada dadewa ba za ta sanar da wuraren da jama’a za su sayi kayan abinci, Magunguna da za a yi amfani da su domin yin sayayya.
Sai dai Gwamnan ya bayyana cewa za a bari Bankuna su yi aiki domin Gwamnati za ta ci gaba da biyan Albashi daga ranar Litinin din nan mai zuwa domin jama’a su samu sayen kayan abinci.
Sai kuma Gwamnan ya kara da cewa Gwamnati za ta iya barin masu sayar da ruwa su ci gaba da sana’arsu amma tare da shawara da kuma kulawar masana harkokin lafiya.
Gwamnan ya kuma tabbatar wa manema labarai cewa za a bari su ci gaba da gudanar da ayyukansu na rahotanni da sauransu ba tare da tsangwama ba.
Ya kuma ja hankalin sauran kananan hukumomi 31 da su hanzarta daukar matakan kula da shiga yankunansu domin dakile yaduwar cutar Covid – 19 a Jihar.
Gwamnan ya kuma ja hankalin jama’a kan bukatar yin addu’o’in hana yaduwar wannan cuta ta Covid – 19 da ake kira Korona.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.