Home / Lafiya / Masari Ya Rufe Wani Gidan Maganin Gargajiya A Dutsi

Masari Ya Rufe Wani Gidan Maganin Gargajiya A Dutsi

Imrana Andullahi

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya rufe wani gidan da ake tsare da mutane da sunan ana yi masu maganin gargajiya a kauyen Tashar Wali cikin karamar hukumar Dutsi a Jihar katsina.

Gwamnan a lokacin wata ziyarar da ya kai wurin bayan dawowarsa saga garin Daura nan take ya bayar da umarnin a dakatar da yin dukkan abin da ake yi da sunan maganin gargajiya a wannan cibiya.

Gwamnan ya kuma bayar da umarni nan take ga Kwamishinan kula da kananan hukumomi na Jihar Alhaji Ya’u Umar Gwajo gwajo da ya mika gayyata zuwa ga mai rikon shugaban karamar hukumar ta Dutsi da kuma Marusan katsina Hakimin Dutsi domin a tabbatar da ikirarin da mai wannan wurin magani ya yi cewa suna sane da aikinsa a wurin.

“Malam Sada Salisu ya tabbatarwa da Gwamnan cewa mahukunta a karamar hukumar na sane da zamansa tare da ayyukan da yake yi a wurin”.

Gwamnan dai tare da tawagarsa sun dauki lokaci sosai suna zagaya gidan da ake ajiye da jama a wai ana yi masu magani inda duk baki dayansu suka ganawa idanunsu irin tanajin da mutanen ke ciki na rashin tsafta da rashin yakamata.

A wani Dakin da Gwamnan ya leka dole ya dawo baya saboda irin warin da yake fita daga dakin.

Da Gwamnan ya tambayi Malam Sada Salisu kome me cikin dakin babu wata gamsasshiyar amsa daga wurinsa.

Gwamnan ya kuma yi mamakin wani mutum da ya fito daga cikin dakin da ya ce shi mai mukamin ASP na Yan Sanda ne da (aka boye sunansa) ya ce ana yi masa magani ne amma gashi ya fito daga cikin daki mai warin gaske.

Da yake magana da Gwamnan mai.maganin ya kafe cewa kwarin da yake fita daga dakin wai saboda rubutun da aka yi ne na Alkur ani da yake yi yana wanke wa ya kuma ce musamman mata da ba su da lafiya su sha da nufin samun lafiya.

Gwamnan ya kuma lura da cewa masu kai ziyara a wannan wurin na karewa da kamuwa da rashin lafiya domin ko wurin kashi irin ramin kasa na gargajiya babu a wurin.

Lokacin ziyarar dai an samu daruruwan mata a cikin wannan cibiyar an kuma tarar da maza kalilan lokacin da Gwamnan ya kai ziyarar.

About andiya

Check Also

Our Mandate Is To Organise Congresses, Says Labour Party Transition Committee Chairman, Umar

  Former president of the Nigerian Labour Congress, NLC, and Transition Committee chairman of the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.