Home / Labarai / Mata Na Bayar Da Yayansu Ga Yan bindiga Saboda Talauci – Hafsat Baba

Mata Na Bayar Da Yayansu Ga Yan bindiga Saboda Talauci – Hafsat Baba

Daga Imrana Abdullahi
Kwamishinar kula da jindadi da walwalar jama’a ta Jihar Kaduna Hajiya Hafsat Muhammad Baba, ta bayyana cewa wasu mata da ke fama da tsananin Talauci na bayar da yayan da suka haifa ga yan bindiga domin samun kudi
Hakika wasu mata na mikawa yan bindiga yayan da suka Haifa a matsayin neman samun kudi, wanda hakan na nufin yin musaya kenan su karbi kudi.
Hafsar Baba ta bayyana hakan ne a wajen taron tattauna abubuwan da suka shafi mata karo na 22 a ranar Laraba da Alhamis ta gabata a Abuja,ta ce abu ne mai muhimmancin gaske a tattauna irin abubuwan da suka shafi mata, musamman yadda mata ke bayar da yayansu mata ga yan bindiga domin kudi wanda hakan ya shafi yaya mata.
Kwamishinar ta ci gaba da cewa faruwar hakan na haifar da cikas ga ci gaban yaya mata ta yadda za a samu ingantaccen tsaro a makarantu, kuma iyayen da ke aika yayansu domin yin aikatau a gidaje da kuma tallace- tallace hakan na taimakawa wajen samun yaya matan da ba su zuwa makaranta.
“Kamar yadda alkalumma daga asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF), Kawhi 60 na sama da miliyan 10 na yaran da ba su zuwa makaranta a Najeriya mata ne”, inji Hafsat Baba.
Ta kuma koka game da halayyar iyaye a kan yayansu musamman ta yadda za su samu ingantacciyar rayuwa.
“Ya dace mu tattauna a game da batun harkar rashin tsaro, don haka ina batun masu kai wa yan bindiga da sauran yan Ta’adda bayanan sirri? duk da a cikin mutane suke,suna bayar da bayanai ga yan bindiga saboda sun mayar da hakan kasuwanci.
“Naga wasu matan da ke bayar da yayansu ga yan bindiga,suje suna kwana da yan bindiga domin kawai su samu kudi.Wannan da an tabbatar da ingancin faruwarsa domin ya faru kuma ba dai- dai bane”, inji ta.
“Idan ka duba a kan titunan mu, za a ga kananan yan mata da ya dace su kasance a makaranta,amma suna ta yawo da yar haka a makale, to amma abin bakin cikin shi ne irin wadannan yaran a yanzu su ne aka dogara da su a cikin iyalansu.
“Ban da batun matsalar tsaro ma akwai na kananan yara da ke yawo a kan tituna suna neman ko za su samu kananan ayyuka.Ga kuma masu daukar kananan yara mata daga cikin al’ummarsu ,daga Jihohinsu zuwa wata Jihar daban su zamo masu rainon yara, suna yin Shara da kuma Dafa abinci.
Duk hakan na hana su zuwa makaranta, kuma hakan na tabbatar da cewa yaya matan ba su da tsaro. Idan taro karami ya zamo shi ne abin da ake takama da shi a cikin iyalin da ya fito,to meye amfanin iyayensa? Domin meye haki8n da ya rataye a wuyan iyayen?
“Duk irin wadannan abubuwan ne ya dace mu zauna mu kuma lura da su a tsanake.Shin ta yaya suke shafar yaya mata? Kuma ta yaya suke shafar iyalin baki daya? Kuma duk irin kokarin kawo daukin da za mu yi dole ne sai mun yi koyi ga kowane dayan mu.
“Sai mun tashi tsaye baki dayan mu domin ganin mun tsare yayan mu, tsaron yayan zai hada ne a makaranta da kuma cikin gidaje.Da iron matsalar tsaron da ake fama da shi a halin yanzu,hakan sai zama tamkar wata fadakarwa ga iyaye su kara tashi tsaye anmatsayin mu na Gwamnati, Iyaye da shugabannin jama’a da addini. Harkar tsaro abu ne da ya rataye a wuyan kowa, idan ba tsaro yayan mu ba za su iya zuwa makaranta ba”, inji kwamishina.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.