Home / Labarai / Matsalar Manoma Da Makiyaya Ta Fi Ta Boko Haram

Matsalar Manoma Da Makiyaya Ta Fi Ta Boko Haram

Matsalar Manoma Da Makiyaya Ta Fi Ta Boko Haram
Imrana Abdullahi
Sakamakon irin bazuwar da tashe tashen hankulan da ake samu tsakanin bangarorin Manoma da Makiyaya har ya fi matsalar da ke cikin Yakin da ake samu na Boko Haram
Sarakuna, Manoma da Ma’aikatan Gwamnati duk su na da hannu wajen matsalar Labuka da Burtalolin Shanu suka haifar da rikicin Manoma da Fulani da ake ciki a halin yanzu.
Fasto Yohanna Y D Buru shugaban wata kungiyar da ke kokarin Farfado da zaman lafiya da dai- daitawa tsakanin Juna ta kasa ne bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manoma labarai a Kaduna.
“An dannewa Fulani hakkinsu a game da Burtaloli da Labuka domin ni na san tun a shekarar 1970 na San akwai hanyar da shanu suke bi tun daga garin Kwai hanya ta ta fi zuwa Jere daga Kwai har zuwa Bauchi ta kai har kasar Kamaru duk Fulani na da wannan hanyar kar yadda kowa ya sani, amma a yanzu duk wadannan hanyoyin wucewar Shanun babu su duk wasu sun Kwace”, inji Fasto Buru.
Ya ci gaba da cewa tun a shekarun 1970 da 1980 duk idan Fulani sun yi wa Manomi barna da gangan ko da kuskure su na biyan diyyar da aka Dora masu tun zamanin ana maganar Fam ne na Ingila ba a batun naira sam
“Shin wai a yanzu babu filayen da ake da su na Gwamnati da ba a komai da su, wanda ana iya mayar da wuraren Gonaki to me ya kawo batun matsalar manoma da makiyaya, saboda ba Gonakin da za a Noma”.
Mutane uku ne keda laifi wajen kwace Burtaloli da hanyoyin shanu na farko Manoma na biyu Sarakuna sai na Uku Gwamnati duk suke da laifi wajen sayar da Labuka da Burtaloli
“Yan siyasa,Sarakuna da Malaman addini ne ya dace su fahimtar da jama’a kowa ya san batun zaman lafiya, amma maganar su na yi.
Ya kara da cewa “Ban ce Fulani basa laifi ba fa don haka a dai duba daga ina matsalar ta fara tun asali.
“Ina matukar jin tsoron abin da yake faruwa a halin yanzu game da batun manoma da makiyaya in har aka kasa samun mafita to yaushe za a yi Noma, in ba Noma ina batun wadatar abinci a kasa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.