Assalamu Alaikum
Da farko ina amfani da wannan lokaci na taya duk al’ummar Musulmi farin cikin zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah SAW, wacce gwamnatin tarayyar Najeriya a jiya ta ware a matsayin rana ta musamman don tunawa da ita.
Annabi Muhammadu SAW shi ne mafi kaunarmu a duniya, bawan Allah da muke shaukin samun cetonsa a lahira. Hallita ta kebantacciya a gurin Allah da muke kokarin koyi da ita. Allah ya kara wa Manzon Allah SAW daraja da wasila fil Jannati.
Haka kuma ina amfani da wannan dama na sanar da ‘yan uwa da dangi na siyasa da masoya a ko ina dangane da halin da jam’iyyarmu ta APC ke ciki a jihar Kano.
Ni Sanata Ibrahim Shekarau, na jagoranci wasu daga cikin wadanda aka zabe mu, daga majalisar kasa. Mun shigar da kuka ga uwar jam’iyya akan rashin gudanar da abubuwan da suka shafi jam’iyya tare damu. Mu zababbu ne, jama’armu suna da hakki. An karbi korafinmu da mutumtawa, kuma mun gode. Muna fatan a warware takaddamar cikin lumana.
Ina sanar da duk jama’armu, ina cikin jam’iyyar APC daram-dam, zamu tsaya har illa Masha Allahu. A wannan tafiya tamu babu cin mutunci, babu zagi, ba wulakanci. Mun yi hakuri amma ba zamu lamunci sakarci ba. Korafinmu yana gaban mahukunta. Ba zamu saurari kowa ba sai wadanda muka kai musu kuka.
A jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam’iyyar APC zababbe a gurinmu. Muna yi masa addu’ar Allah ya karfafi zuciyarsa kuma Allah ya taya shi riko. Sauran wadanda aka zabesu tare da shi su 35 muna addu’ar Allah ya yi musu jagora.
Allah ya taimaki Najeriya
Allah ya taimaki jihar Kano
Allah ya taimaki jam’iyyarmu ta APC
Allah ya yi riko da hannun shugabanninmu
Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya
Nagode
-MIS
Sanata Ibrahim Shekarau
Sardaunan Kano