Home / Labarai / Minista Hadi Sirika Ya Tallafawa Mutanen Daura Da Miliyan 11

Minista Hadi Sirika Ya Tallafawa Mutanen Daura Da Miliyan 11

Mustapha Imrana Abdullahi

Ministan kula da harkokin ma’aikatar zirga zirgar Jiragen sama na tarayyar Nijeriya Sanata Hadi Sirika ya tallafawa mutane  Daura da kudi naira miliyan Goma sha daya domin rage masu radadin zaman gida sakamakon Sanya dokar zaman gida dare da rana domin hana yaduwar cutar Covid – 19 da ale kira Korona bairus.

Kamar yadda bayanai suka zi saga karamar hukumar Daura inda aka yi rabon kudin an ruwaito cewa yin hakan bai ransa nasaba da kara inganta tattalin arzikin mutanen karamar hukumar ta Daura.

Za kuma a Raba kudin ne miliyan sha daya a daukacin mazabun karamar hukumar Dauraguda Goma sha daya.

Alhaji Aliyu Lawal ne ya wakilce shi domin rabon kudin kuma daga cikin mutanen da suka shaida rabon kudin sun hada da dan majalisar dokoki na Jiha mai wakiltar Daura honarabul Nasiru Yahaya Daura da kuma tsohon kantoman Daura honarabul ABBA Mato Tate da shugabannin jam’iyya da sauran jama’a da dama.

Dan majalisar mai wakiltar Daura ya bayyana farin cikinsa a madadin al’ummar Daura baki daya.

About andiya

Check Also

Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya koka kan matsalar tsaro a jihar Katsina, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.