Home / Labarai / Zan Yi Karatun Azumin Ramadana Ne A Bauchi – Shaikh Dahiru Bauchi

Zan Yi Karatun Azumin Ramadana Ne A Bauchi – Shaikh Dahiru Bauchi

Kamar yadda dimbin al’umma a ciki da wajen Nijeriya suka dade suna jiran samun matsaya game da karatun da shaikh Dahiru Usman Bauchi ke gudanarwa a kowace shekara a lokacin watan Azumin Ramadana a yanzu an samu cimma matsaya game da Tafsirin bana wanda Sheikh Dahiru Bauchi ya saba yi a Kaduna duk Shekara.

Shaikh Dahiru Bauchi ya tabbatar wa manema labarai  cewa Insha Allahu a bana za’a gudanar da Tafsirin ne a Bauchi ba tare da an je Kaduna ba.

 

Shehin Malamin yace za’a yi amfani da kafafen yada labarai daga Kaduna da sauran manema labarai  daga wurare daban daban In da za su dauki Tafsirin a watsa a Duniya domin amfanin jama’a kamar yadda aka dade ana karantar da dimbin al’umma tsawon shekaru

 

Sannan Malamin yaja hankalin cewa kar a daina Sallar Juma’a akalla mutum goma sha biyu hakanan Sallar Tahajjudi da Asham, a samu koda mutum bakwai zuwa sama a dinga gudanar da Sallah.

 

Bauchi yace ayi hakuri da yadda Allah ya kaddara lamarin, Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya Albarkan manzon Allah s.a.w.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.