Home / Labarai / Mun Gamsu Da Taron Jin Ra’ayin Jama’a Domin Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Gaya

Mun Gamsu Da Taron Jin Ra’ayin Jama’a Domin Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Gaya

Mustapha Imrana Abdullahi
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da ya jagoranci taron jin ra’ayin jama’a domin sako duba kundin tsarin mulki ya bayyana cewa hakika sun Gamsu da irin yadda jama’a suka nuna sun san kundin tarin mulkin Nijeriya.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna jim kadan bayan tashi taron karbar jin ra’ayin jama’a da ya gudana a garin Kaduna.
Sanata Kabiru Gaya ya ci gaba da cewa mutane daga bangaren kungiyoyin kwadago, masu zaman kansu har ma da masu bukatar a kara kirkiro masu Jihohi duk sun kawo bukatunsu tun a wannan rana ta farko, wanda hakan na tabbatar da cewa jama’a sun samu cikakkiyar masaniya a kan wannan lamari na gyaran kundin mulkin tsarin kasa da rabon da a ta ba shi tsawon kusan shekaru Ashirin tun shekarar 1999 sai yanzu da majalisa ke yin yunkurin hakan.
Sanata Gaya ya bayar da misali cewa kamar shi ya na wakiltar kananan hukumomi 16 ne daga Jiha mai kananan hukumomi 44 wato Jihar Kano, amma sai ga wasu da suke da kananan hukumomi 8 kawai kuma yankunan sanatocinsu uku kamar Jihar Kano, wanda idan aka yi duba sosai Jihar Kano za a iya fitar da karin Jihohi biyu daga cikinta.
“Saboda haka an samu mutanen da ke son a kara kirkiro masu Jihohi daga cikin wadanda suke da su a halin yanzu. Kuma duk za mu tattara bukatun nasu mu kuma kai wa majalisa, muna fata a samu dai – daito da majalisar Wakilai ta yadda al’amura za su ta fi bai daya”, inji Sanata gaya.
Ya kara da cewa an shirya irin wannan taron ne a kowace shiyyar kasar nan za a yi shi a wurare biyu kamar wannan shiyyar Arewa maso Yamma ana yi nan a Kaduna da Sakkwato kuma an tsara ne ta yadda jama’a na can kasa za su fahimci me ake son yi wanda a halin yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu kusan kowa tun daga can kasa kasa ya fahimci komai ana kuma saran samun nasara.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.