Honarabul Bara’u Yusuf Mai Kawai Dikko, Kansila Mai Kula da bangaren lafiya na karamar hukumar Funtuwa ya bayyana cikakkiyar gamsuwa, murna da farin ciki a game da irin yadda aka nada masu BA shugaban karamar hukumar Shawara har mutum 50.
Honarabul Bara’u Yusuf Mai Kawai Dikke ya bayyana hakan ne a lokacin da Yake tattaunawa da Manema labarai a harabar karamar hukumar da ke garin Funtuwa, kuma Sakamakon adalci irin na shugaban karamar hukumar Funtuwa ya sa har ma kudin watan baya ma duk za a BA su.
” Yin hakan zai taimaki karamar hukumar Funtuwa ya Kara saituwa domin akwai mutanen kirki da aka zaba don su bayar da Shawara GA shugaban karamar hukumar domin ci gaba da Raya karamar hukumar komai ya ta fi lafiya.
Honarabul Bara’u Yusuf Dikke, ya kuma Kara da shaidawa Manema labarai cewa, “tun daga ranar da aka ce an Kaddamar da mu a matsayin kansiloli a karamar hukumar Funtuwa kuma ni in Kula da bangaren lafiya hakika ban zauna ba, kullum muna Shiga lungu da sako ina duba shin ina inda asibitoci suke da suke bukatar Gyara KO wata kulawa.
Ya ce Sakamakon hakan mun gano asibitoci da dama da ke bukatar a Gyara su da nufin a Raya su al’umma sun ci gaba da amfana, kuma muna yi wa Allah godiya domin duk mutumin da ke a karamar hukumar Funtuwa ya GA irin yadda Ake ta gudanar da ayyuka a cikin garin Funtuwa da dukkan sassan karamar hukumar Baki daya a cikin duk har da asibitoci.
“Kuma a yanzu haka ina tabbatar maka cewa tun da aka fara sai muka ga ya dace mu ba shugaban karamar hukumar Shawara a Kan mutane masu fama da larurar Karzuwa,Kirci da dai Sauran wadansu kuraje da muke bin lunguna da sakuna inda almajirai suke da Ake ganin su kamar BA su da galihu muna binsu makarantu mu gano matsalolinsu da larurorinsu muna yi masu magunguna ana BA su magani tare da yi masu aikin da ya dace domin ceton lafiyarsu. Sannan mu a karamar hukumar Funtuwa a shirye muke a taimakawa duk Wanda keda karancin yadda zai taimaka wa kansa da batun magani duk muna tsaye tsayin daka muga komai ya Kara inganta ta wajen taimakawa Jama’a. KO a yanzu kafin inzo wannan wurin yanzu haka sai da na je na bayar da Kudi naira miliyan daya GA wani malami da ke Bagari da ya samu Karaya guda hudu a jikinsa,wannan malamin suna yin karatun Alkur’ani suna yin WA kasa addu’u’a don haka idan an bar Shi a zugunme kamar an tsugunnar da karamar hukumar Funtuwa ne,Amma rayuwarsa na amfanar karamar hukumar Funtuwa da kasa Baki daya matuka Gaya Kadan kenan daga cikin abin da muke yi a takaice a karamar hukumar Funtuwa”, Inji Honarabul Bara’u Yusuf Dikke Mai kwai
“Hakika ina matukar murna da farin cikin wannan taron da aka yi domin Kaddamar da wadannan mutane su 50
THESHIELD Garkuwa