Home / Labarai / MUNA BUKATAR JIRAGEN YAKI – SANATA MANDIYA

MUNA BUKATAR JIRAGEN YAKI – SANATA MANDIYA

 

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Sanata mai wakiltar yankin Funtuwa ta Kudu da ake kira Karaduwa a Jihar Katsina  Sanata Bello Mandiya, ya bayyana matukar damuwarsa da irin yadda yan bindiga ke kai hare hare suna kwashe jama’a a wasu sassan yankunsa da nufin karbar kudin fansa.
Sanata Bello Mandiya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban majalisar Dattawa, inda ya tashi tsaye a doron majalisa ya ce hakika muna bukatar Jiragen yaki domin magance matsalar yan bindiga masu satar jama’a su na Garkuwa da su.
“Muna bukatar Jiragen yaki saboda irin abin da ya faru a Ruwangodiya da ke cikin karamar hukumar Faskari a wannan yankin da nake yi wa wakilci ya bayyana a fili sai an kara matsa kaimin magance wannan matsalar”.
Sanata Adamu Aliero ya bayyana cikakken hadin kai da goyon bayan a dauki matakan magance irin wannan matsalar.
Haka zalika Sanata Barkiya saga Jihar Katsina ya tofa albarkacin bakinsa game da wannan matsalar inda ya dan yi tsokacin yadda ya dace a magance matsalar.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.