Home / Kasashen Waje / Muna Cikin Jimami, Bakin Ciki Da Rashin Jindadi Kuma Muna Bakin Ciki Da Hakan – Yan Nijar Mazaunan Kaduna

Muna Cikin Jimami, Bakin Ciki Da Rashin Jindadi Kuma Muna Bakin Ciki Da Hakan – Yan Nijar Mazaunan Kaduna

….Juyin mulki ba alkairi ba ne
Daga Imrana Abdullahi
Daukacin al’ummar kasar Nijar mazauna Jihar Kaduna sun bayyana bakincikinsu da tsananin rashin jindadinsu da abin da ke faruwa a kasar Nijar.
Don Allah a duba Allah da sayayyar Manzon Allah SAW sojojin nan su mayar wa da zababben shugaban kasa Muhammad Bazoum da kujerar shugabancin da yake yi wa al’ummar kasar Nijar.
Bashir Sahabi wani dan asalin kasar Nijar ne mazaunin Kaduna ya tattauna da wakilin mu ya manhajar whattsapp a madadin yan kasar Nijar mazaunan Kaduna da ke arewacin Najeriya
“Saboda haka muna bakin ciki muna kuma yi wa kasar mu addu’a sai dai kawai mu nemi zaman lafiya da kwanciyar hankali kawai, a bisa hakan muna kira ga sojoji da su yi wa Allah su mayar ma wannan bawan Allah da yake da kishi tare da yi wa Nijar aiki tukuru da Mulkinsa kamar yadda jama’ar kasa suka taru suka zabe shi ya zama shugaban kasa”.
” Duk mai son kasa da ke kishin Nijar ba zai so irin hakan ta rika faruwa ba saboda kowa ya Sani juyin mulki ba alkairi ba ne, saboda haka muke yin kira ga daukacin jama’a da su yi kishin kasa ta yadda za su rika yin alfahari da ita. Mun Sani hakika wannan zababben shugaba da wasu sojoji ke cewa sun yi masa juyin mulki ya yi kokari kwarai domin ya samar da abubuwa da yawa na ci gaban yan Nijar ba kamar yadda lamarin yake ya can baya ba har kasar ma ta sake sosai ba kamar da ba domin har masu neman kudi zuwa suke yi a cikin Nijar. Kuma hatta mu yan Nijar da muke zaune a kasashen waje koke – koken da muke samu a yanzu duk ya yi mana sauki ba kamar da ba har ma a yanzu sai muje gida kuma har mu samu gudinmawa daga can ba kamar da ba, shi ya sa muke cewa”.
Saboda haka muke yin kira ga wadannan sojojin da suka ce sun yi juyin mulki da su yi wa Allah da son Manzon Allah SAW da malaman mu da iyaye da kakanni da ayi hakuri a mayarwa wannan mutum mai kishin kasa da Mulkinsa a zauna lafiya domin ita duniyar nawa take? hakika muna jaddada cewa muna bakin cikin hakan na mu jin dadin wannan juyinn mulkin saboda muna son mulkin Dimokuradiyya. Ko gobe muna alfahari da shugaban kasa Bazoum, bisa hakan ne yasa muke cewa mayar masa da Mulkinsa domin shi adalin mutum ne ko yau ko gobe har jibi ma muna tare da Bazoum muna kuma kaunarsa muna tare da shi a koda yaushe fatan mu kawai a mayar masa da kujerarsa. Kuma mu ba mu son a kawo mana fitina Ko a hargitsa mana kasa a dai yi komai cikin ruwan sanyi, kuma muna yin kira da babbar murya cewa suk kasashen Afirka gaba daya a zauna lafiya domin mu samu ci gaba da karuwar arziki”.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.