Home / Labarai / Muna Fata Allah Ya Inganta Najeriya – Sanata Kawu Sumaila

Muna Fata Allah Ya Inganta Najeriya – Sanata Kawu Sumaila

Bashir Bello Majalisa Abuja

Sanata Abdultahman Kawu  Sumai’la ya bayyana bukatar da ake da ita ga yan Najeriya da su rika Sanya kishin kasa da tsoron Allah a cikin zukaransu a wajen aiwatar da dukkan komai da nufin ci gaban kasa da kowa ke bukata.

Sanata Kawu Sumai’la ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce komai za a canza ko a yi da zarar babu shi har cikin zukatan yan kasa da kowa zai kudiri aniyar alkairi lallai lamarin ba inda za a je koda kuwa an canza taken Najeria kamar yadda aka yi a halin yanzu.

Kawu Sumaila ya ci gaba da bayanin cewa abin da aka yi na canza taken Najeriya aiki ne a majalisa da aka kawo kudiri kuma majalisar ta amince bayan an bi dukkan matakan da ya dace a bi, saboda an ga shi ne ya fi cika da inganci a kan taken kasa da ake rerawa a yanzu don haka ana fatan Allah madaukakin sarki ya ci gaba da yi mana jagora a koda yaushe”.

About andiya

Check Also

NA 8 Div Sokoto new GOC,  General Ibikunle assumes

S. Adamu, Sokoto A new GOC for the 8 Division Nigerian Army, Sokoto , appointed …

Leave a Reply

Your email address will not be published.