Home / Ilimi / Muna Kwana Da Tashi Da Matsalar Ilimi A Jigawa – Gwamna Badaru

Muna Kwana Da Tashi Da Matsalar Ilimi A Jigawa – Gwamna Badaru

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana cewa babbar matsalar da suke kwana da tashi da ita itace ta inganta harkar ilimi a Jihar Jigawa.
Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin tattaunawa na rediyon bbc hausa.
Gwamnan ya ce ta yaya za a dauki mutum aikin koyarwa, amma sai kawai mutum yaki zuwa aiki ya yi zamansa a gida.
“A kan irin wadannan matsaloli ne da wadansu masu tarin yawa  da muka dauki matakan gyarawa ne wasu mutane suka ga ya sabawa abin da suke bukata a cikin zukatansu”.
Saboda haka wannan matsala ta gyaran ilimi a Jihar Jigawa muna kwana da tashi da ita a koda yaushe.
Sai kuma babbar matsala ta biyu da muke kokarin ganin mun samar da hanyoyin rigakafi sun haka da batun harkar man fetur.
” Domin a Jihar Jigawa babbar hanyar samun kudin Gwamnati itace ta Gwamnatin tarayya da ake samu a wata wata, kuma mun san irin yadda man fetur zai kasance ko yau ko Gobe, saboda ko a kwanan nan an ga yadda man ya kasance a kasar Amurka da wasu wurare a lokacin batun kulle saboda cutar korona”.
Ya kara da cewa muna kara kokarin inganta hanyoyin sana’o’i da Noma da Kiwo da muke Tallafawa jama’ar Jigawa ba tare da nuna wani bambanci ba.
Gwamna Badaru ya kuma bayyana aniyarsa domin ganin ya gano babban dalilin da yasa ake samun matsalar rashin samun magungunan Mata da Kananan yara a Jihar.
” Ina samun korafe korafen cewa ba’a samun magungunan kananan yara da mata a wasu wuraren duk da tsarin bayar da kudin sayen magungunan domin a samu a wadace, da na karbi mulki a Jigawa mun tarar cewa ana bayar da naira miliyan 15 ne wai don a sayi Magunguna irin wadannan amma na ce Bana son jin irin wannan maganar, sai aka kawo mini cewa a wadace ko’ina ya samu in bada naira miliyan 75 nan da nan da mika kudin ba tare da yin wani lissafi ba, saboda wasu na kira na mai Kalkuleta to babu wani lissafi da nayi nake biyan kudin amma ta yaya za a ce ba a samun magungunan
Ya bayar da tabbacin cewa zai bincika lamarin in ma ta kama ya kara kudin ne duk zai yi domin amfanin jama’a.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.