Home / Kasuwanci / MUNA MARABA DA MASU ZUBA JARI A JIHAR NASARAWA – Salihu Enah

MUNA MARABA DA MASU ZUBA JARI A JIHAR NASARAWA – Salihu Enah

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Kwamishinan ma’aikatar ciniki, masana’antu da zuba jari na Jihar Nasarawa, Salihu Ali Enah, ya bayyana cewa sun yi kyakkyawan ingantaccen tsarin maraba da dukkan kamfanoni da masu son zuba Jari a Jihar.
Kwamishina Salihu Ali Enah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin ranar Jihar Nasarawa a kasuwar duniyar kasa da kasa a Kaduna.
Kwamishinan ya ce Gwamnatin da Gwamna Injiniya Abdullahi Sule ke yi wa jagoranci a Jihar Nasarawa na da sahihan tsare tsaren rungumar duk wani kamfani ko mutumin da ke son zuba jari a Jihar.
Kwamishina Salihu Enah ya ci gaba da cewa muna shaidawa dukkan mai son zuba jari a Jihar Nasarawa cewa an tanaji yadda komai zai kasance a cikin sauki.
“Jihar Nasarawa wuri ne da Allah ya albarkace su da dimbin ma’adinai da duniya ke nema don haka wuri ne mai ni’ima
Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a wadanda suka samu halartar kasuwar baje kolin ta kasa da kasa da ke Kaduna da su ziyarci rumfar Jihar Nasarawa a kasuwar domin su ganewa idanunsu irin abubuwan da Jihar ta baje kolinsu a kasuwar, domin samun damar garabasar da ke Jihar ta fuskar zuba jari a bangaren ma’adinai da sauran sana’o’i daban daban.
Kwamishinan ya kara da cewa Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya bayar da uzurinsa a game da kasuwar baje koli ta Bana da ya ce yaso ya samu zuwa da kansa amma saboda al’amarin kamfe na zaben da ke tafe bai samu dama ba, amma ya na ba masu zuba jari tabbacin cewa akwai romo sosai a Jihar ga masu son zuba jari a Jihar.
Da yake tofa albarkacin bakinsa babban Sakatare a ma’aikatar ciniki da masana’antu na Jihar Nasarawa Rilwanu Alqasim Ibrahim, cewa ya yi duk da dokar da ta hana Jiha ta shiga zundum baki daya a cikin al’amarin masana’antu, amma dai akwai muhimmanci da Gwamnati ke ba masu zaman kansu.
“Saboda haka ne idan kun saurari jawabin da kwamishina ya gabatar ya ce Gwamnati ta yi kamfanin Taki amma sai aka bayar da shi ga masu zaman kansu kuma hakan ya faru ne domin a karfafa Gwiwar masu zaman kansu a harkar masana’antu tare da yin la’akari da irin tanajin kafa masana’antu, hakika akwai tanaji mai kyau ga duk masu zaman kansu”.
Babban sakataren ya kuma bayar da misali cewa ba abin mamaki ba ne idan an samu Mai a Jihar Nasarawa domin yanayin da ya taso tun daga Abakalike ya taho zuwa ga yankin Kogin Banuwai har zuwa Nasarawa da Gombe duk abin daya ne don haka ba wani mamaki akwai albarkatun Mai a wurin, don haka akwai dimbin ma’adinai a Jihar Nasarawa da Allah ya albarkaci Jihar da su”.
A kasuwar baje kolin Jihar Nasarawa  sin baje kolin kayayyaki kamar ma’adinai da Allah ya albarkaci Jihar da su, kayayyakin da aka kera a Jihar da suka hada da Gadajen asibiti irin na zamani, kayan amfanin Gona da kamfanonin sarrafa kayan amfanin na Gona da kayan da aka samar ta hanyar gargajiya da sauransu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.