Home / Ilimi / Muna Neman Dalibai 333 – Gwamna Masari

Muna Neman Dalibai 333 – Gwamna Masari

Muna Neman Dalibai 333 – Gwamna Masari

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya shaidawa tawagar Gwamnatin tarayya da suka zo Katsina domin jajantawa mutanen Jihar Katsina game da sacewa a lokacin da aka tarwatsa daliban makarantar sakandare ta GSSS  Kankara cewa ya zuwa yanzu suna nan suna neman dalibai dari uku da Talatin da uku da kodai an sace su ko kuma suna wurin iyayensu.
Masari ya ce ya zuwa yanzu dai a wannan makaranta akwai dalibai Tari Takwas da Talatin da Tara (839) ne yasa aka gano cewa a yanzu ana neman dari 333 saga cikin yawan daliban.
Tawagar Gwamnatin tarayyar ta Isa Katsina ne karkashin jagorancin mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro Babagana Manguno, da suka zo domin yin jaje a game da lamarin.
Massri ya shaidawa Tawagar Gwamnatin tarayyar cewa har yanzu ba su yi magana da kowa ba ” babu wani ko gungun wadansu mutanen da muka yi magana da su cewa su ne suka aikata wannan mugun aikin”. Inji Masari.
Da yake tofa albarkacin bakinsa ministan tsaro Bashir Magashi ya bayyana cewa ba za su bari masu irin wannan aikin na aika aika  ba su samu sukunin ko minti daya.
Ya kuma jajantawa jama’ar Jihar katsina da yan uwa da abokan arzikin iyayen daliban da lamarin ya shafa

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.