Home / KUNGIYOYI / Mata Na Jagorantar Zanga Zanga A Kankara  

Mata Na Jagorantar Zanga Zanga A Kankara  

Mata Na Jagorantar Zanga Zanga A Kankara

Mustapha Imrana Abdullahi
A garin Kankara hedilwatar Karamar hukumar Kankara da ke cikin Jihar Katsina dimbin Daruruwan Mata sun fito domin jagorantar Zanga Zanga game da batun sace masu yaya da aka yi a wata makarantar sakandare da ke garin.
Su dai matan da kuma wadansu Mazaje na komawa ne da irin yadda matsalar tsaro ke kara yin kamari a Jihar.
Faruwar wannan Zanga Zanga ya biyo bayan irin yadda a Daren shekaran jiya wadansu mahara dauke da miyagun bindigogi a kan Babura suka je makarantar GSSS da ke Kankara suka yi awon gaba da dalibai masu yawa inda wadansu kuma da dama suka tarwatsa cikin daji, amma daga baya an samu nasarar gano wasu daga cikin daliban wasu kuma suna can hannun yan bindigar cikin Daji.
Koda yake wadansu bayanai da ba a tabbatar da su ba na cewa jami’an tsaro sun gano maboyar inda suka kai daliban a yanzu kuma wai har an yi masayar harbe harbe da yan bindigar da jami’an tsaro.
Za dai mu kawo maku yadda lamarin yake kayawa nan gaba kasancewa muna nan muna bibiyar labarin.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.