Related Articles
...A Guji Butulci Da Cin Amana
Daga Imrana Abdullahi
WATA gamayyar al’ummar mutanen kauyukan da suka fito daga Jihar Zamfara sun yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Muhammad Bello Matawalle da ya tabbatar ya rike mutanen Kauyuka da hannu biyu domin samun nasara.
Mutanen da suka fito daga Kauyukan Jihar Zamfara sun ce babbar bukatar da suke yi wa Gwamnan ita ce ya rika su riko na kirki ka da ya bari a samu wani gurbin da Iska za ta shiga ko kadan tsakanin Juna
Mutanen sun bayyana hakan ne ta bakin Alhaji Nasiru Karfa, Dan Galadiman Karfa makaman Nasarawan mai layi kuma Sarkin Yakin Dan Galadiman birnin Magaji Alhaji Ibrahim Dan Galadiman birnin Magaji dan malikin birnin Magaji,lokacin da suke ganawa da wakilin mu a garin Gusau hedikwatar Jihar Zamfara
“Gwamna ya rike mu hannu biyu kuma muma mu rike shi da hannu biyu har Allah ya sa mu kai gaci wato nasara ta samu kamar yadda ake bukatar a samu”.
Sun kuma yi kira ga sabon zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya rike batun harkar tsaro da kyau domin al’ummar kauyuka su yi Noma sosai kamar yadda suke bukata a wadata kasa da abinci.
Dan Galadiman Karfa ya ce ya na son yin jan hankali ga Gwamnan Jihar Zamfara da sauran jama’ar Jihar da babbar murya cewa duk abin da mutum zai yi a duniya ya guji abubuwa biyu mutum lallai ya guji butulci ya guji cin Amana.
“Ni a iya sanina abubuwan da Gwamnan ke yi a cikin garin Gusau hedikwatar Jiha ba duk sauran kauyuka ake yi wa shi ba, amma a yanzu an yi zabe mun ba Gwamna goyon baya sauran kananan hukumomi 13 amma yanzu ana ta ce mana wai yan gudun hijira ne suka yi zabe. Saboda haka ai mutanen kauyuka ne yan gudun hijira suka yi zaben kuma ko gobe da yardar Allah muna sanar da mutanen Gusau cewa mu kauyawa kuma ko yau yanzu mun dauki matakin cewa za mu ci gaba da ba Gwamna kuri’ar mu da nufin a samu nasara domi ba wata dabarar da za su bi”.
Kuma muna son Gwamnan Jihar Zamfara ya dubi sakataren jam’iyyar APC na Jihar Zamfara Alhaji Ibrahim Umar Dan galadiman birnin Magaji kuma dan malikin birnin Magaji, da idanun rahama saboda a duk shiyyarsa babu inda aka samu faduwa ko gaira kuma a duba irin yadda a rufarsa da sauran rumfuna ya Sanya masu kuri’u kaf baki daya don haka a duba shi sosai.
A kuma taimakawa sauran kananan hukumomi Goma sha uku kamar yadda tsarin mulkin kasa ya amince a taimaka a duba a gani wane wuri ne ya kawo masa kuri’a? Amma ba za ta yuwu ba mai cin Dunya daban mai bakin baki kuma daban. Mu ke zabe inda Gwamna ya ce ayi zabe kuma ko batun S. A da ya dauka da sauran masu mukamai ai sun fi dubu hudu (4000) idan an duba a karamar hukumar Birnin Magaji babu babban sakatare ko daya kuma ina son a duba rumfar Karfa duk wanda ya tsaya takarar nan tun daga shugaban kasa da sauran yan majalisu sai da na ba su kuri’a dari 377 kowanensu a cikin akwatin Karfa tun daga Sanata Bola Tinubu, dan majalisar tarayya da Sanata Sahabi Ya’u duk sai da na ba su wadannan kuri’u, don haka ba gudu ba ja da baya.