Home / News / Mune Kan Gaba A Fannin Noma – Babangida Mu’azu

Mune Kan Gaba A Fannin Noma – Babangida Mu’azu

Tsohon Gwamnan Jihar Neja Dakta Aliyu Babangida Mu’azu kuma shugaban gidauniyar tunawa da marigayi Sardauna ya bayyana cewa tsarin noman shinkafar da ake tafiyarwa a fadin tarayyar Nijeriya zai kai kasar ga samun nasarar da kowa ke bukatar ya gani.
Aliyu Babangida Mu’azu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a kaduna Jim kadan bayan kammala babban taron da cibiyar tunawa da sardauna ta shirya inda aka tattauna yadda za a ciyar da Noma gaba, ta fuskar kasar da ya dace ayi amfani da ita da kuma samar da ingantaccen iri da malaman Gona.
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu a wajen taron gidauniyar tunawa da sardauna
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Munnir Yakubu lokacin da yake jawabi a kan irin nasarorin da suka samu a fannin Noma
Ya bayyana irin kasidar da tsohon Gwamnan Adamawa Murtala Nyako ya gabatar a kan yadda Noma da Kiwo zai ci gaba a matsayin abin farin ciki na annashuwa ga manoma da yan kasa baki daya.
“Hakika nan gaba zai zama Nijeriya ce ke samar da shinkafa a duk fadin Afirka baki daya, saboda irin tsare tsaren da ake yi suna samar da nasarar da za ta yi jagoranci ga samun hakan a nan gaba kadan”.
Ya kuma kara Ankara da Gwamnati tare da sauran yan kasa baki daya da cewa ta yaya zamu ki bayar da tallafi ta fuskar Noma amma su wadanda suke fadin hakan suna bayar da tallafi a kasashen su, saboda haka a kula da wayon da ake kokarin yi mana don kawai mu rika zuwa kasashensu mina Sayo abincin da zamu ci.
Ya ci gaba da cewa dukkan kasidun da aka gabatar a halin yanzu a wajen wannan taro za su tattare dukkan bayanan baki daya su kuma gabatar da su ga cibiyoyin Noma, Manyan makarantu da dukkan inda ya dace domin samun ci gaba harkokin Noma baki daya.
Wadanda suka samu damar halartar taron sun hada da mataimakan Gwamnan Kaduna da katsina, Alhaji Munnir Jafaru Yariman Zazzau da kwamishinonin Noma ma Jihohin Jigawa,Neja da katsina da suka gabatar da jawabai kan irin nasarorin da jihohinsu sula samu a harkar Noma
Tsohon Gwamnan Jihar Neja Dakta Aliyu Babangida Mu'azu yake ganawa da manema labarai a kaduna
Tsohon Gwamnan Jihar Neja Dakta Aliyu Babangida Mu’azu yayin ganawarsa da manema labarai a kaduna
Da yake gabatar da kasida tsohon Gwamnan Jihar Adamawa ya gabatar da cewa akwai dimbin damar samun ci gaban Nijeriya ta hanyar Noma da Kiwo idan aka yi amfani da dimbin arzikin da ake da shi a fadin kasar baki daya.
Ya kuma ce a Adamawa sun samar da katafaren Dam da za a iya yin amfani da shi domin samar da hasken wutar lantarki, amma saboda halin ki in kula har yau Dam din na nan.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.