Home / Big News / Mutane 2 Sun Mutu A Bikin Aure A Katsina

Mutane 2 Sun Mutu A Bikin Aure A Katsina

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanai daga rundunar yan sanda a Jihar katsina na cewa sakamakon yin abinci da aka yi da Ruwan Zakami ya haddasa mutuwar mutane biyu a karamar hukumar Mani cikin Jihar Katsina.
Kamar yadda rundunar yan sandan ta bayyana cewa sun samu kiran waya daga babban Jami’in yan sanda da ke karamar hukumar Mani wato (DPO) cewa wani Musa Suleiman mai shekaru 25 da ke kauyen Ali Yaba, cewa sun hada kai da wata da ake kira Shafa’atu Sirajo mai shekaru 20 da ke zaune a wannan garin sun hadu sun sa Zakami a cikin abincin da aka rabawa baki a wajen bikin Aure da ya yi sanadiyyar haifar masu da shiga cikin halin dimauta da rashin lafiyar da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane biyu.
A cikin wata sanarwar da ke dauke da jami’in hulda da jama’a na rundunar a Katsina SP Gambo Isa ya ce Babban jami’in yan sanda da ke Mani ya hanzarta daukarsu zuwa babban asibitin Mani, inda aka tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu mutanen sun hadar da Bilkisu Surajo mai shekaru 20 sai kuma Ibrahim Sani dan shekara 13 dukkansu da suka zo daga kasar Nijar duk an tabbatar da sun mutu yayin da sauran ake duba su a asibiti.
Dukkan wadanda ake zargi da aikata wannan laifi ta hanyar hadin baki Musa Suleiman da Shafa’atu Sirajo tuni yan sandan sun kama su kuma sun tabbatar da aikata hakan

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.