Home / Ilimi / Mutane 25 Da Wamakko Ya Dauki Nauyin Karatunsu A Jami’ar Benin Sun Karbi Shahadarsu

Mutane 25 Da Wamakko Ya Dauki Nauyin Karatunsu A Jami’ar Benin Sun Karbi Shahadarsu

Daga  Imrana Kaduna
Mutane Ashirin da biyar da suka kammala karatunsu a jami’ar jamhuriyar Benin da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya dauki nauyin karatunsu sun kammala kuma sun karbi takardar kammalawar a Sakkwato.
Dukkansu da suka hada da mace guda daya sun samu nasarar kammala karatun masu tare da samun kyakkyawan sakamakon digiri mai daraja ta daya ko kuma mai daraja ta biyu.
Darussan da suka koya sun hada da karatun sanin kimiyyar halittu, Kemistry, kimiyyar samun bayanai, karatun aikin jarida, karatun na’ura mai kwakwalwa da karatun samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashe da harkokin Difilomasiyya.
Da yake jawabi a wajen taron mikawa wadanda suka kammala karatun shahadarsu Sanata Wamakko, da ke wakiltar mutanen yakin Sakkwato ta Arewa cewa ya yi ilimi ne babban abin da za a iya barwa jama’a gado musamman matasa da zai daga darajarsu.
Kamar yadda ya bayyana ilimi ne abin da zai taimakawa mace ko namiji ya zama mai amfani a cikin al’umma baki daya.
Wamakko wanda ya samu wakilcin tsohon kwamishinan harkokin addini, Furofesa Musa Garba Maitafsiri, Sanata Wamakko ya yi alkawarin ci gaba da irin wadannan ayyukan ci gaban jama’a, har tsawon rayuwarsa.
Daraktan kula da harkokin mulki a Ofishin Sanata Wamakko Alhaki Almustapha Alkali,ya ce da akwai wadansu daruruwan daliban da aka dauki nauyin karatunsu kuma Sanata Wamakko ne yake dauka suna karatunsu a ciki da wajen Jihar a Nijeriya.
Alkali ya kuma yi kira ga matasan da suka kammala karatun masu da su zama jakadun Wamakko a cikin al’umma iyalansu, Sakkwato, Nijeriya da sauran wuraren gudanar da rayuwa baki daya.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko a kan harkokin kafafen yada labarai Bashir Rabe Mani, da aka rabawa manema labarai.
Mai magana da yawun iyayen wadanda suka yi karatun Alhaji Sanusi Abubakar godiya ya yi ga Wamakko bisa wannan gagarumin nauyi da ya sauke masu a matsayinsu na iyaye ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da suyi koyi da abin da Wamakko ke yi domin daga darajar al’umma.
Da yake jawabi a madadin wadanda suka yi karatun Sani Magaji, bayuana farin cikinsa ya yi ga shugaban kwamitin tsaro na majalisar Dattawa kuma mataimakin shugaban kwamitin yaki da batun cin hanci da karbar rashawa inda ya yi addu’ar ci gaba da samun daukaka daraja da martaba ga Sanata Wamakko.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.