Home / Labarai / Mutane 43 Ba Talatin Ba, Sun Mutu A Harin Yan Ta’adda A Goronyo – Tambuwal

Mutane 43 Ba Talatin Ba, Sun Mutu A Harin Yan Ta’adda A Goronyo – Tambuwal

Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta tabbatar cewa an kashe mutane 43 ba Talatin ba a lokacin harin da yan bindiga suka kai garin  Goronyo  da ke karamar hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya tabbatar da  hakan bayan gudanar da binciken kwakwaf game da mutanen da suka mutu a harin da yan bindiga suka kai kasuwar Goronyo ranar Lahadin da ta gabata.
Kuma bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mai ba Gwamnan shawara a kan harkokin kafofin yada labarai Muhammadu Bello da aka rabawa manema labarai.
Tun da farko dai Gwamnan sai da ya fayyace cewa mutanen sun kai 30, lokacin da shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya Janar Farouk Yahaya ya kai masa ziyara.
“Yawan mutanen da suka mutu a Goronyo; ina bayanin cewa sun haura Talatin. Don haka ban bayar da tabbacin ko mutane nawa ba ne.
“A yanzu muka kammala taro da masu ruwa da tsaki kuma na tabbatar da cewa mun rasa mutane 43 abin bakin ciki a wannan matsalar harin, inji Gwamna Tambiwal.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kuma yi addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka Rigamu gidan gaskiya

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.