Home / Ilimi / Mutane Dubu 11, 350 Suka Rubuta Jarabawar Tantance Malamai Ta Kasa

Mutane Dubu 11, 350 Suka Rubuta Jarabawar Tantance Malamai Ta Kasa

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna. Arewacin Najeriya

Magatakardan hukumar yi wa malamai rajista na kasa Farfesa Josiah Ajiboye ya ce akwai mutane dubu 11, 350 da suke rubuta jarabawar tantance malamai a kashi na farko da ake yi a ranar Asabar da ta gabata a duk fadin tarayyar Najeriya.

Farfesa Adebiye, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zagayawa domin duba aikin da makarantar Sascon,da ke Maitama cikin garin Abuja, daga irin sakon da ake samu a duk fadin kasa na nuna cewa aikin rubuta jarabawar na samun gagarumar nasara da ci gaban da ake bukata tun daga yawan masu rubuta jarabawar da kuma tantance su.

Ajiboye, wanda ke tare da babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya David Adejo, ya ce ” a halin yanzu dai a dukkan fadin tarayyar Najeriya muna da yawan masu rubuta wannan jarabawa mutum dubu 11, 350 da suke rubuta jarabawar, inda Jihar Legas ta fi ko’ina yawan masu rubuta jarabawar domin suna da mutane dubu 1, 500 da wani abu, sai kuma Jihar Kano da babban birnin tarayya Abija; sannan akwai Jiha kamar Kebbi Kebbi suka kasance masu karancin yawan masu rubuta jarabawar.

”Hakika akwai ci gaba kwarai koda ta hanyar batun tantancewa ne, saboda daga cikin abin da muka yi shi ne mun samar da wani dandalin yanar Gizo domin ya ba mi damar samun tantance duk wanda zai rubuta jarabawar, kuma tsarin na aiki kwarai.

Muna iya duba sunanka da hoton ka karami da zai fito a ko’ina? domin ta haka ne za mu tabbatar da cewa mutanen da suke rubuta jarabawar sune ainihin wadanda suka rubuta neman za su yi jarabawar domin ta ta fi kamar yadda ya dace.

Ya kuma yi bayanin cewa jarabawar ana yin ta ne a kowace jiha da ke fadin tarayyar Najeriya, da idan lokacin farawarta ya yi ake yi daga ranar Laraba a kammala ranar Juma’a.

Da yake jawabi a game da batun kokarin da Gwamnatin tarayya ke yi na kakkabe matsalar malaman da ba su cancanta ba, cewa ya yi daya daga cikin muhimman hanyoyin da suke no domin magance matsalar a fannin koyarwa ita ce ta ganin kowa ya rubuta jarabawa domin babu wanda zai samu lasisin koyarwar ba tare da ya rubuta jarabawar neman cancanta ba.

Ya ce; ” koda kai Farfesa ne a jami’a,dole ne kawai ka rubuta wannan jarabawar kafin ka samu wannan takardar shedar ta makanta da kuma lasisin koyarwa. Kuma wani abu da muke yi a wannan fannin shi ne Sanya idanu ga makarantu sannan kuma muna da hanyoyin gudanar da bincike a kan satifiket, domin tabbatar da nagartar su baki daya.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.