Home / KUNGIYOYI / Sanata Abdul’Aziz Yari Ne Ya Dace Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa – Gamayyar kungiyoyi 593

Sanata Abdul’Aziz Yari Ne Ya Dace Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa – Gamayyar kungiyoyi 593

Muna goyon bayan Sanata Yari ya zama shugaban majalisar Dattawan Najeriya
Daga  Imrana Abdullahi, Kaduna, Arewa maso Yammacin Najeriya
Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu karkashin jagorancin kungiyar National Concensus Movement (NCM) guda 593 da ke arewacin Najeriya sun bayyana wa manema labarai cewa suna tare da kokarin da Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari ke yi na son zama shugaban majalisar Dattawa ta tarayyar Najeriya karkashin majalisa ta Goma (10).
Shugaban kungiyar Northern concensus movement (NCM) na kasa kwamared Dokta Abdullahi Aliyu, karkashin gamayyar kungiyoyi masu rajista 593 sun shaidawa wani taron manema labarai da aka yi a Kaduna cewa su a matsayinsu na yan arewacin Najeriya sun amince su goyawa Sanata Abdul’Aziz Yari baya dari bisa dari domin ya zama shugaban majalisar Dattawa ta Goma da za a rantsar nan gaba kadan.
Kwamared Abdullahi Aliyi ya ci gaba da bayanin cewa suna yin aiki a kan dukkan shugabannin addini, dukkan shugabannin arewacin Najeriya da duk wani mai ruwa da tsaki a yankin ya goyi bayan kokarin da Sanata Abdul’Aziz Yari yake yi na zama shugaban majalisar Dattawan Najeriya domin hakan shi ne mafita.
“Gamayyar kungiyoyin karkashin Kwamared Abdullahi Aliyu, sun bayyana dalilansu kamar haka suna yi ne sakamakon irin yawan tarin kuri’un da yankin Arewa ya bayar da ya bayar da yawan kashi sama da Sittin na yawan kuri’ar da Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayar har ya lashe zaben shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, sannan kuma Abdul’Aziz Yari ya bayar da gagarumar gudinmawa wajen samun nasarar lashe zaben shugaban kasa da APC ta yi a Jihar Zamfara duk hakan ya taimaka kwarai”.
Saboda haka mu dukkan mu muna kallon lamarin da cewa lokaci ne ya yi da za a saka mana bisa irin kokarin da yankin Arewa ya yi kuma sayayyar shi ne a ba mu shugaban majalisar Dattawan Najeriya karkashin Sanata Abdul’Aziz Yari, Shetiman Zamfara.
“Yankin Arewa dai na cewa a koda yaushe muna son siyasar samun gaskiya da adalci a koda yaushe”.
“Baki dayan wadannan kungiyoyi masu rajista da hukumar yi wa kungiyoyi rajista ta kasa su 593 da suka hadu a kan gamayyar kungiyar NCM duk ba su amince da a rika yin siyasar addini ba, ko siyasar bambancin yare ko domin wani bangaranci na kasa ba kawai abin da ake so shi ne siyasar wa ya fi yawa da kuma bayar da kuri’ar da aka samu nasara har aka kafa Gwamnati kawai illa iyaka”.
“Kuma ai kamar yadda kowa ya Sani a cikin tsarin Dimokuradiyya babu inda aka yi maganar addini kawai batu ne na wa ya fi yawan kuri’a kawai, in kuma mutum bai amince da wannan maganar ba sai ya je ya duba tsarin. Sannan min kawo wannan maganar ne domin kawai wani mai tambaya a wannan wurin ya yi tambaya a kai domin ba batun da ya kawo mi kenan ba”. Inii Comrade Abdullahi Aliyu.
Imrana Abdullahi Northwestern Nigeria.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.