Home / Labarai / Mahaifin Tabuwal Ya Rasu Yana  Da Shekaru 96 A Duniya

Mahaifin Tabuwal Ya Rasu Yana  Da Shekaru 96 A Duniya

Gwamna  Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi rashin mahaifinsa wanda da ya shafe shekarru 96 a duniya, Shaikh Haruna Waziri Usman yaya ne ga mahaifin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

 Muhammad Bello mashawarci ga gwamna a kan harkokin yada labarai ya fitar da sanarwar rasuwar wadda aka rabawa manema labarai a jihar Sakkwato ya ce Allah shi ne mallakin komai  da haka yake sanar da rasuwar mahaifinsa Shaikh Haruna Waziri Usman.

Ya ce Margayin ya rasu ne a gidansa da ke garin Tambuwal a ranar Alhamis yana da shekarru 96, a duniya.

Shehi shi ne jagoran darikar Tijjaniya a garin Tambuwal gaba daya, ya yi wa addinin Allah hidima sosai al’ummar  garin Tambuwal da jihar Sakkwato musamman mabiya darikar Tijjaniya sun yi rashin gwarzo mai son taimakawa addinin musulunci.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.