Home / Labarai / Na Amince Da Dakatar Da Sarkin Zurmi – Gwamnan Zamfara

Na Amince Da Dakatar Da Sarkin Zurmi – Gwamnan Zamfara

 Imrana Abdullahi
Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!
A cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun Kabiru Balarabe, mai rikon mukamin sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Bello Mohammad Matawallen Maradun, MON (Shatiman Sakkwato, Barden Hausa) tuni ya amince da Dakatar da Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar Muhammad nan take, an kuma Sanya Alhaji Bello Suleiman (Bunun Kanwa) ya rike jagorancin masarautar ba tare da bata lokaci ba.
Haka kuma Gwamnan ya amince da Sanya wani kakkarfan kwamitin bincike domin ya bincike zargin da ake yi wa dakataccen Sarkin, na hannu a cikin yaduwar ayyukan ta’addancin yan bindiga a masarautar, don haka ba sunayen yan kwamitin binciken kamar haka.
1 – tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Muhammad a matsayin Shugaba
2- tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara Muktar Ahmad Anka, Mamban kwamitin
3 – Honarabul Faruku  Musa Dosara = Mamba
4 – DIG mai ritaya Mamman Tsafe mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin tsaro = Mamba
5 – Honarabul Yusuf Abubakar Zugu mai bayar da shawara a kan harkokin Masarautu = Mamba
6 – Wakilin Yan Sanda = Mamba
7 – Wakilin Yan Sandan Farin kaya DSS = Mamba
8 – Wakilin jami’an Sibil Difens = Mamba
9 – Musa Liman Shinkafi babban Sakatare a ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida = Sakataren kwamitin
An kuma ba kwamitin wa’adin sati uku ya kammala aikinsa ya kuma gabatar da rahotonsa.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.