Home / Big News / Na Shiga Cikin Farin Ciki Sosai Matuka Da Diyata Ta Haddace Littafin Allah – Shaikh Musa Asadussunnah

Na Shiga Cikin Farin Ciki Sosai Matuka Da Diyata Ta Haddace Littafin Allah – Shaikh Musa Asadussunnah

Daga Imrana Abdullahi
Shaikh Musa Yusuf Asadussunnah ya bayyana cewa ya shiga cikin matukar farin ciki da annashuwar da ba ta da iyaka ranar da yarsa da ya haifa ta haddace littafin Allah.
Shaikh Asadussunnah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala yin saukar mahaddatan inda yarsa mai suna Habiba Musa Yusuf Asadussunnah, ta ba shi wata kyautar yaba wa da murna ta musamman tare kuma da wadansu malamanta duk suma ta ba su kyautar.
“Hakika wannan ranar da yar da na haifa ta haddace littafin Allah na samu kaina a cikin farin ciki mara iyaka don haka ina yi wa Allah madaukakin Sarki godiya”.
Sai ya yi kira ga daukacin iyayen yara da su sani cewa duk abin da ƴaƴansu za su karanta a duniya bai kai littafin Allah Alkur’ani ba, don haka abin ayi murna da farin ciki ne kwarai.
“Duk abin da a yanzu za ta karanta a rayuwarta ribar kafa ce don haka nake yin alfahari da wannan ranar kuma ba zan manta da ita ba, daman daya daga cikin burukan da nake da shi, shi ne in ga ta haddace Kur’ani kuma ta cika Mani Burina.
Ya kuma bayyana murnarsa a fili da irin yadda jama’a daga ko’ina suka halarci wurin saukar mahaddata da aka yi a Kaduna tun daga kan mai girma Gwamna har kowa ga kuma irin yadda wannan dakin taron yake sai an sanya makudan kudi amma ga shi a nan aka yi wannan taron mahaddata, musamman kuma a makarantar da a yanzu ne take neman matsuguni inda za a gina makarantar.
Saboda haka irin yadda dakin taron nan ya cika muna yi wa kowa godiya da fatan alkairi, yadda kowa yazo wurin nan lafiya Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

About andiya

Check Also

Dangote, Pope Leo XIV, Trump, Xi Jinping, others Named in TIME 100 Most Influential People for 2026

  Renowned African industrialist and philanthropist, Aliko Dangote, has been named among TIME Magazine’s 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.