Home / News / NA YI IMANI DA KASA DAYA AL’UMMA DAYA – ANYIM PIUS ANYIM

NA YI IMANI DA KASA DAYA AL’UMMA DAYA – ANYIM PIUS ANYIM

 

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

 

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Sanata Anyim Pius Anyim ya bayyana cewa ya amince tare da yin Imani da Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya al’umma daya.

Sanata Anyim Pius Anyim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa shugabanni da masu zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Kaduna.

Anyim Pius ya ce a halin yanzu abin da Najeriya ke bukata shi ne Gwarzon shugaban da zai hada kan Najeriya  ta yadda kawunan jama’a za su ci gaba da dunkule domin samun nasarar da kowa ke bukata.

“Na yi karatu na a Najeriya duk yaya na da na haifa su na cikin Najeriya kuma a nan suke yin karatunsu ban kuma ta ba yin tafiyar sati biyu ba na Najeriya ba duk inda na je kafin sati biyu na dawo gida, ba kuma da na ko daya da yake zaune a wata kasa”.

Anyim Pius ya ci gaba da cewa “Na san Kaduna tun a shekarun baya da suka gabata lokacin akwai wani dan uwana da ke aiki a masakar Kaduna a lokacin na san daga wurin titin Jirgi kasa na unguwar Kakuri mutum zai ga irin yadda ma’aikatan kamfanoni da masakun da ke Kaduna suke kwararowa ka san a Najeriya akwai abin yi, amma a yanzu lamarin ya zama sai tarihi kawai”.

To, da na zama shugaban kasa zan fara da kokarin Farfado da masana’antun da suka durkushe kuma zan samar da wasu sababbi domin jama’a su samu sukunin dogaro da kansu a koda yaushe, domin na amince da kasa daya al’umma daya.

“Tun da na zama shugaban majalisar Dattawa tun daga nan ba a sake cire shugaban majalisa ba domin na duba yadda lamarin yake na kuma tabbatar da gyaran da ya dace ayi, akwai lokacin da aka zo Mani da batun matsalar ruwan jami’ar Ahmadu Bello Zariya nan take na ce wa wanda ya zo Mani da maganar zan kai ka wurin shugaban kasa kuma haka aka yi, a yanzu Ahmadu Bello Zariya na da babban Dam din ta na kanta da take samar da wadataccen ruwan sha da sauran ayyukan da ake yi na gudanar da harkokin rayuwa.

Haka zalika a lokacin da muke cikin Gwamnati na Sani mun yi tsari mai kyau domin matatar mai ta Kaduna kuma har mun bayar da aikin kwangilar, amma bayan mun bar Gwamnati ban san abin da ake cikin ba a yanzu.

“Na ji mutane na cewa PDP ta dawo kuma yayan jam’iyyar APC na cewa Shugaba Jonathan ya dawo to wannan shi ne halin da ake ciki fa”, inji Anyim Pius Anyim.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.