Home / Big News / Nenadi Ba Shugabar Jam’iyya Ba Ce – Umar Mai Rakumi

Nenadi Ba Shugabar Jam’iyya Ba Ce – Umar Mai Rakumi

Daga Imrana Abdullahi
…Tuni jam’iyyar Lebo ta daukaka kara
Alhaji Umar Ibrahim Taba Mai Rakumi, Sakatare na kasa baki daya na jam’iyyar Lebo, ya yi karin bayani a game da batun cewa Sanata Nenadi ce shugabar jam’iyyar ta kasa inda ya ce suma a matsayinsu na shugabannin jam’iyyar na kasa labari kawai suka ji cewa Kotu tayi wani hukunci da ya ba Nenadi da shugabannin rikon da suke tare  da ita cewa ta ci gaba da gudanar da jam’iyyar Lebo har zuwa lokacin da za a yi babban taron jam’iyyar na kasa.
“To wannan hukuncin da Kotu ta yanke abin mamaki ne tun da ita kanta kotun ba ta ma da hurumin ta saurari kara irin wannan na rikita rikitar shugabancin jam’iyya, Kotun koli ce ta bayar da wannan hukuncin ba wata kotu har ita Kotun Kolin da ta isa ta shiga cikin harkar shugabancin jam’iyyu na siyasa, na biyu kuma kotun Kolin ta yanke hukuncin cewa a wata karar da ita kanta Nenadin ce ta kai karar har zuwa Kotun koli amma kotun ta ce babu wani hurumin da suke da shi dama za su kai wannan karar. Sannan jam’iyya ta koma gida ta tattara jama’arta su zabi shugabanninsu wannan shi ne abin da yake kamar yadda tsarin mulkin jam’iyyar ya zayyana din haka muke yin mamakin yadda shi wannan alkaluma ya dauki wannan hukuncin ya yanke shi, amma duk da ba mu samu ainihin takardar hukuncin daga kotu ba na yadda aka yi shari’ar a yanzu Lauyoyinmu suna nan har sun rubuta daukaka kara neman kotu ta dakatar da wannan hukuncin kuma hukumar zabe kada ma ta yi amfani da shi hukuncin, tun da daman ainihin karar hukumar zabe aka kai kuma ita hukumar zaben ta ce Nenadi ba ta da hurumin kai wannan karar kuma su hukumar zabe INEC ba su ma san da ita ba.
“Don haka ba abin da ya dace mu tayar da hankali mu ba ne kuma ba abin da ya dace ya’yan jam’iyya su tayar da hankalinsu ba ne.
Don haka ina yin kira ga magoya baya da yan jam’iyyar mu da su kwantar da hankalinsu kamar yadda kotu ta yi hukunci a baya ta tabbatar da shugabancin jam’iyya a inda ya dace din haka wannan hukuncin kotun ba zai tabbata ba Sam za a yi watsi da shi.
Sai dai Sakataren jam’iyyar Lebo na kasa Umar Mai Rakumi ya ce duk da sun san hukuncin da Kotun koli ta yanke tun a can kwanan baya, amma dai wajibi ne idan an kai kara kotu sai a amsa kiran kotun wannan shi ne ya sa har jam’iyyar Lebo ta halarci duk zaman kotun da aka yi bayan Sanata Nenadi ta kai kara don haka ne muka je muka kuma kare kan mu a kotun don gujewa yanke hukuncin kotu kada ya hau kan mutu, shi ya sa Lauyoyin jam’iyya suka je kotun kuma sun gaya wa kotu duk hujjojin da ake da su na kada kotu ta saurari karar.
Na farko Lauyoyin mu sun shaidawa alkaluma cewa bai ma kamata ya saurari karar ba, na biyu kamata ya yi ya sani cewa abin da Kotun koli ta yanke hukunci a kai bai dace shi ya yi magana a kai ba domin ba kotun da ta isa ta yi magana a kansa ba, idan ma akwai abin da ba fahimta a kai ba sai a koma can kotun Kolin domin ta yi bayani ko warware abin da take nufi da hukuncin da ta yanke a kan duk wata karar da aka kai ta yanke hukunci. Kamar dai abin da kowa ya sani ne kawai abin da ke faruwa a cikin kotuna kowa ya sani alkali ya yi abin da ya ga dama amma tun da ba shi ne kotun karshe ba mun daukaka kara kuma mun roki a dakatar da hukuncin har sai abin da Kotun gaba ta ce a kan karar.

About andiya

Check Also

Why Yakubu Dogara Is Claiming Nigeria Is On The Right Track

By Imrana Abdullahi Nigeria is drowning while Rt. Hon. Yakubu Dogara smiles from the comfort …

Leave a Reply

Your email address will not be published.