Home / Labarai / NUJ Ta Karrama Muhammad Rabi’u Musa

NUJ Ta Karrama Muhammad Rabi’u Musa

Mustapha Imrana Abdullahi
Sakamakon irin kokarin taimakawa rayuwar al’umma ba tare da nuna bambanci ko gajiyawa ba ya sa kungiyar yan jaridu ta kasa (NUJ) reshen kamfanin wallafa jaridun New Nigeria da Gaskiya Ta Fi Kwabo suka ga dacewar Karrama Alhaji Muhammad Rabi’u Musa da lambar girmamawa domin kara masa kwarin Gwiwa ya ci gaba da abin da yake aikatawa.
Alhaji Muhammad Rabi’u Musa dai ya kasance mutum ne mai kokarin taimakawa wajen inganta rayuwar al’ummar kasa da suka hada da daukar nauyin  koyawa jama’a sana’o’i, biyawa dimbin yara kudin rubuta jarabawar NECO da WAEC tare da biya masu kudin jarabawar JAMB da kuma nema masu makarantar gaba da Sakandare domin su zurfafa karatunsu ta yadda za su zama abin alfahari a cikin al’umma.
Shi dai Rabi’u Musa mutum ne da ya shahara wajen kokarin Sanya farin ciki ga marayu da sauran marasa Galihu da ke cikin al’umma.
Ga shi kuma dan kasuwa mai kokarin fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiya.
Ya kuma kasance ya na aiwatar da dukkan wadannan ayyukan ciyar da rayuwar marasa karfi gaba ne kamar yadda ya shaidawa manema labarai cewa ya gada ne daga wurin mahaifinsa don haka aikin taimakon rayuwar jama’a abu ne da ya dade ya na samun natsuwa da farin ciki sakamakonsa.
“Kamar yadda binciken yan jarida na nuna ya kan yi taimakon ne ba tare da nuna wani bambancin kabila, addini ko wani bangaranci na ya na kokarin yi ne kawai domin Allah”.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.