Home / Labarai / SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KADUNA TA AREWA YA GABATAR DA KASAFIN KUDIN SHEKARAR 2022 NA  KUDI N4.7BN GA KANSILOLINSA

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR KADUNA TA AREWA YA GABATAR DA KASAFIN KUDIN SHEKARAR 2022 NA  KUDI N4.7BN GA KANSILOLINSA

 

Shugaban zartarwa na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Hon. Mukhtar Lawal Baloni ya sabunta tsarin majalissar kananan hukumomi tare da gabatar da kudi naira biliyan bakwai da digo (N4.7bn) na kasafin kudin shekara ta 2022 ga ‘yan majalisar domin amincewa.

 

 

Bayanin hakan na kunshe  ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun  Abdullahi Ibrahim Jami’in Yada labarai na Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da aka rabawa manema labarai.

 

Shugaban ya gabatar da kudirin kasafin kudin a gaban majalisar dokokin kananan hukumomi wanda shugaban majalisar, Hon. Umar Ilyasu.
Shugaban ya gabatar da kudirin kasafin kudin a gaban majalisar dokokin kananan hukumomi wanda shugaban majalisar, Hon. Umar Ilyasa.

Ya ce sabunta tsarin majalisar shi ne tabbatar da hadin kai na gaskiya da kuma ci gaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa a harkokin gudanarwar kananan hukumomin.

 

 

 

Da yake jawabi a lokacin gabatar da kudirin kasafin kudin, shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa, an shirya kasafin Naira biliyan 4.7 tare da shigar da bukatun jama’ar Kaduna ta Arewa daga sassa daban-daban na karamar hukumar.

A cewarsa, za a yi amfani da kasafin ne da kason kananan hukumomi daga Gwamnatin Tarayya, da kuma kudaden shiga na cikin gida (IGR) na majalisar ya ce, majalisar na shirin samar da kudaden shiga na cikin gida na Naira biliyan 1.4 a cikin 2022, Don samar da walwala ga al’ummar karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

 

 

 

Balano ya ce, ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da tsaro ne za su samu kaso mafi tsoka na kasafin kudin da aka gabatar a gaban majalisar, yayin da kuma za a baiwa mata da matasa fifiko a kasafin kudi na shekarar 2022.

 

Da yake karbar kasafin, shugaban majalisar, Umar Iliyasu ya ce, ‘yan majalisar dokokin kananan hukumomin za su binciki kasafin kudin da kuma tabbatar da cewa an zartas da shi cikin gaggawa, da kuma ganin yadda ayyukan kananan hukumomin ke ci gaba da gudana ba tare da wani bata lokaci ko matsala ba.

 

 

Shugaban majalisar ya sake cewa suna aiki tare da rundunar zartaswar kananan hukumomin domin tabbatar da ganin an samar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Kaduna ta Arewa.

 

 

Haka kuma, yayin da yake zantawa da manema labarai a harabar majalisar dokokin jihar Kaduna, sakataren kansilan karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Hon. Mustapha Abubakar Zukogi ya yaba da kokarin Shugaban Karamar Hukumar na sauya Kasafin Kudi na 2022 domin inganta rayuwar al’ummar Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, musamman ta Mata da Matasa da kuma samar da ci gaba mai kyau a Karamar Hukumar.

 

 

Kuma ƙaddamar da kasafin kuɗin shekarar 2022 ya kasance ranar Juma’a 31st/12/2021.

 

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.