Home / Labarai / Rufe Wani Ofishi Ba Saboda Lauyan Shekarau Ba Ne – Gwamnatin Jihar Kano

Rufe Wani Ofishi Ba Saboda Lauyan Shekarau Ba Ne – Gwamnatin Jihar Kano

…..Mai Ginin Ofisoshin ya kasa biyan kudin harajin kasa na shekaru biyar duk da gargadi da aka yi masa
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa wani kakkarfan kwamitin karta kwana ne da ke aiki a game da batun masu amfani da Filaye a Jihar Kano ne ya rufe wani ginin da ke kan titin Murtala Muhammad cikin garin Kano wanda ginin na dauke da Ofisoshi da yawa har da ofishin lauyan da ya samu nasara a shari’ar da aka yi ta jam’iyyar APC game da zaben shugabannin mazabu.
A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ta yi bayanin cewa sabanin irin yadda wasu kafafen yada labarai na yanar Gizo suka rika yin bayani cewa lamarin bashi da wata alaka da rufe ofishin da lauyan da ya samu nasara yake wato a hukuncin da kotu ta yanke.
Ya ce jami’an kwamitin da Gwamnatin Kano ta Sanya domin kula da biyan kudin kasa da suke aiki tare da hadin Gwiwar hukumar kula da biyan kudin haraji ta Jihar Kano su na kan gudanar da aikin su ne domin tabbatar da an biya kudin harajin kasa na Jiha da nufin samawa Gwamnati kudin shiga.
Malam Garba ya bayyana cewa kamar yadda alkalumman da suke da su suka tabbatar daga hukumar shi dai wannan ginin mai lamba kamar haka C14/C16 a kan titin Murtala Muhammad wanda mallakar kamfanin Isyaka Rabi’u & Sons ne amma ba na Lauya  Nureini Jimoh ba wanda kuma kwamitin ya rufe shi bayan an aikawa mai ginin takarda a ranar 14, ga watan Satumba wanda kuma daga baya aka aike masa da takardar gargadi bayan ya kasa yin komai game da bukatar da aka aike masa na ya biya kudin harajin kasa da yakamata ya biya tun tsawon lokacin da ya kai shekaru biyar daga shekarar (2016- 2021).
Kwamishinan ya ci gaba da cewa a lokacin gudanar da aikin kwamitin ne ya rufe wadansu gine- gine gida Bakwai da suka ki biyan kudin harajin na su kuma an yi aikin ne a ranar 1 ga watan Disamba 2021 duk dai a kan titin Murtala Muhammad da ke cikin birnin Kano da kuma wasu sassan Jihar da suka hada da titin gidan Zoo, titin Zariya da kuma titin Inrahim Taiwo a Kano.
Ya bayyana cewa su a iya saninsu, kwamitin ko kuma hukumar da ke kula da batun biyan kudin haraji a Jihar Kano na yi ne da asalin wanda keda wannan ginin ba yan haya ba da suka kama haya a wurin saboda haka ya musanta labarin da wasu kafafen yada labarai suka bayar da ake danganta lamarin da harkar siyasar da ta faru kwanan nan a Jihar.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.