Daga Imrana Abdullahi
A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da aikin gina titunan garin Gusau domin fara aikin sabunta birane da Gwamnatin sa ta bullo da shi.
Sashe na farko na sabunta biranen ya fara ne da gina tituna guda huɗu da ke da nisan kilomita 3.5, gami da inganta mahaɗa da magudanar ruwa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce an gudanar da bikin kaddamar da titinan ne a Gidan Sambo daura da ofishin ‘yan sanda da ke Gusau.
Ya bayyana cewa aikin gina titin yana cikin abubuwan da Gwamna Lawal ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe; don gina hanyoyi da yawa, da kuma inganta hanyoyin zamani da kuma kula da su.
Sanarwar ta kara da cewa “A wajen bikin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa sabunta birane na daya daga cikin manyan abubuwan da Gwamnatin sa ta sa a gaba da nufin magance rashin ci gaba a garuruwa da tun lokacin da aka kirkiro Jihar Zamfara.
“Kashi na farko na aikin ya hada da sake ginawa tare da inganta hanyoyin gari mai tsawon kilomita 3.5 a Gusau, babban birnin jihar, tare da inganta magudanar ruwa.
“Aikin gina titunan zai hada da titin Bello Barau – Titin Tsohuwar Kasuwa, Hanyar Bello Barau – Titin Rundunar ‘Yan Sanda ta Tsakiya, Titin Bello Barau – Titin Gidan Gwamnati, da Kwanar Yan Keke – Fadar Sarki da Titin Tankin Ruwa.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta yi imanin cewa ta hanyar samar da hanyoyin da za a iya isa da kuma dogaro da su, tana samar da yanayin da zai jawo hankulan masu zuba jari, da bunkasa harkokin yawon bude ido, da kuma ba wa ‘yan kasuwa kwarin gwiwa.
“Gwamnan ya kuma bukaci mazauna garin Gusau da su yi hakuri a lokacin da ake gudanar da aikin, inda ya kara da cewa a wasu lokutan ana samun ci gaba na gaske tare da rashin jin dadi na wucin gadi, amma sakamakon zai fi karfin matsalolin.”