Home / Lafiya / Sabuwar Shekarar Musulunci 1444 AH: Ku Ci gaba da yin addu’a, Hadin Kai Da Taimakon Juna Domin Kasar mu Ta Ci Gaba – Ayu Ya Shawarci Al’ ummar  Musulmin Nijeriya

Sabuwar Shekarar Musulunci 1444 AH: Ku Ci gaba da yin addu’a, Hadin Kai Da Taimakon Juna Domin Kasar mu Ta Ci Gaba – Ayu Ya Shawarci Al’ ummar  Musulmin Nijeriya

 

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi a tarayyar Najeriya da su yi amfani da lokutan bikin sabuwar shekarar Musulunci wajen aiwatar da abubuwan da za su sanya gobensu ta yi kyau tare da inganta hadin kai. Ya shawarce su da su ci gaba da yin addu’o’in samun hadin kai, ci gaba da taimakekeniya tare da fahimta a tsakanin Juna.

Bayanin hakan yana kunshe a cikin wata takardar dake dauke da sa hannun Babban mai bayar da shawara ga shugaban PDP na kasa a kan harkokin Yada labarai da Sadarwa, Mallam Yusuf Abubakar Dingyadi, wanda aka rabawa manema labarai.

Takardar ta ci gaba da bayanin cewa yin hakan zai taimaka kwarai a samu shugabanin da za suyi jagoranci wajen samar da zaman lafiya da kuma ci gaban kasa da zai haifar da samun ingantacciyar kasa mai albarka.

“Kada mu karaya mu bari wani ya yi amfani da gazawarsa a lalata kasa don son kai. Mu mun kasance mutane ne da muke a hade tare da juna don haka mu yi kokarin ganin wadanda ke zuwa a gabaninmu sun samu makoma mai kyau. Babu abin da zai canza mana kudirin mu wajen ganin al’ammura sun inganta a kasar mu da muke alfahari da ita”.

“Saboda haka, a madadin daukacin Yayan PDP baki daya, ina taya yan uwana Musulmi maza da mata na kasarnan murnar bikin sabuwar Shekarar Musulunci a shekarar 1444 AH bayan hijira”.

Ayu ya shawarci al’umma Musulmi dasu ci gaba da taimakon juna a tsakaninsu, su kuma ci gaba da yin yafiya tare da sadaukarwa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa a koda yaushe.

Ayu ya kuma yi kira ga jama’a da su taimakawa PDP a matsayin jam’iyyar da ita ce kadai zata ceto kasar ta kuma sassaita harkokin kasar baki daya da suka hada da tattalin arzikin kasa, tsaro, Ilimi da tabbatar da kasa daya al’umma daya a koda yaushe.

Shugaban na PDP ya kuma yi bayanin cewa ya na farin cikin irin yadda ya’yan jam’iyya ke aiwatar da harkokin jam’iyya a kasa baki daya, musamman irin yadda suke bayar da cikakken hadin kai da goyon baya wajen ganin an samar da hamshakiyar kasa.

Sa Hannun

Yusuf Abubakar Dingyadi
Babban Mataimaki Na Mussaman ga
Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa.
30/7/2022

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.