Home / News / Sake Fasalin Kasa: Ya Dace Gwamnatin Tarayya, Masu Babatu Su Cimma Matsaya – Olawepo Hashim

Sake Fasalin Kasa: Ya Dace Gwamnatin Tarayya, Masu Babatu Su Cimma Matsaya – Olawepo Hashim

Sake Fasalin Kasa: Ya Dace Gwamnatin Tarayya, Masu Babatu Su Cimma Matsaya – Olawepo Hashim

 

Mustapha Imrana Abdullahi
Wani dan kasuwa kuma dan takarar shugaban kasa a shekarar 2019 Mista Gbenga Olawepo Hashim ya ce lokaci ya yi da dukkan bangarorin da ke jayayya da Juna da za su dai- dai ta a game da mahawarar da batun sake fasalin Nijeriya domin hakan ya dace ayi shi ne domin hadin kan kasa, zaman lafiya, tsaro da ci gaban kasa baki daya.
A cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin, Olawepo Hashim bayani ya yi cewa tun da dai Gwamnatin tarayya ba za ta ci gaba da yin wani abu ba a game da batun rabon iko a kan wasu al’amura, kuma za a iya samun abin da ake bukata domin abu ne mai yuwuwa, shi kuma bangaren masu daga murya a bangare daya ba wai komai da suke magana a kansa ba ne zai yuwu a cikin jadawalin bukatunsu kafin lokacin zabe mai zuwa hakika ya dace a samu matsaya tsakanin bangarorin.
Kamar yadda babban dan kasuwan ya ce, tsarin dai-daitawa daga wajen majalisar Zartaswa ta fuskar yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska a kan wani bangare da ke magana a game da batutuwan yau da kullum da kuma na bangaren masu yin dokoki, hakika duk za su yuwu musamman a bangarorin da suka kasance daman akwai batutuwa a bayyane da aka cimma yarjejeniya.
Ya bayyana cewa “lokaci ya yi mu amince a kan batutuwan da za a iya amincewa da su sai kuma mu ci gaba da tattaunawa a game da wadanda ba a fayyace su ba, amma za su iya zama cimma nasara a nan gaba. Samun cimma dai-daito ba alama ce ta rauni ba, amma dai alamace da ke nuna cewa ana bukatar ci gaba,da kuma taimakon kasa”.
“Wasu daga cikin wuraren da suke bukatar cimma yarjejeniya ta kasa sun hada da batun kirkirar yan Sandan Jihohi da kananan hukumomi, dai-dai da yan sandan tarayya, domin a samu bangaren tsaron cikin gida mai inganci da zai kara karfin tsaron kasa.
“Gyaran da zai ba kananan hukumomi damar samun mallakar dukkan ma’adinai na kasa musamman ga wadanda suke a kan doron kasa.Samar da gyare gyaren a game da samar da wutar lantarki wato a ba Gwamnatin tarayya da Jihohi ikon samar da wutar lantarki,sarrafata da kuma rarraba wa”, da kuma gyaran fuska a bangaren dokar zabe da suka hadar da samar da sakamakon zabe ta hanyar zamani da na’ura a dukkan matakan da ake tattara sakamakon zabe”.
Wannan abu da muka ambata a sama, baya bukatar wasan kwaikwayo ko kuma bata lokaci ko sai an yi taron kasa.
Mista Olawepo Hashim daga cikin wannan tsarin samar da gyaran tsarin mulki a cikin sauki ya yi bayani cewa zai samu gagarumin goyon baya daga Gwamnonin jihohi 36 a Nijeriya, da kuma shugabannin majalisu dokokin jihohi.
“Abin da ake bukata na samun kashi 2 colin uku na goyon baya daga majalisun  jihohi a fadin kasa baki daya za a iya samunsa domin samun abin da ake bukata a kundin tsarin mulki in an gudanar da gyaran”.
“Dole ne Nijeriya ta ci gaba da zama a cikin zaman lafiya da kyautatuwar al’amura, gina kasa ba zai taba zama ya samu a kwana daya ba ko a lokaci kankani ba. Ai da akwai rayuwa bayan shekarar 2023 kuma ina da tabbacin cewa Nijeriya za ta rayu kuma sauran wadansu batutuwan za a iya duba su bayan zaben 2023 da ikon Allah.
Za.a iya samun dai-daitawa ne idan akwai taarin cimma yarjejeniya na kasa”.
“Tsarin amincewa alama ce da samun kwarin Gwiwa ba rauni ba. Inda kawai na ga ba batun amincewa shi ne abin da masu tsatsatsauran ra’ayi suke ta matsawa sai sun raba  Nijeriya. Don haka daga cikin mutane iri na da muke son Nijeriya da kuma wadanda suka sadaukar da kai ko kuma suka sha wahala domin samar da Dimokuradiyya a kasar nan.
“Hakika wannan lamari ne da magabatan mu suka cimma yarjejeniya a babban taron da aka yi a Lancaster na kasar Amurka a shekarar 1958. Wanda batu ne da marigayi Dokta Nnamdi Azikiwe, shugaban mutanen yankin Kusu maso Gabas da suka halarci taron ya kawo kuma an amince da shi inda baki daya aka amince da ci gaban zaman Nijeriya a dunkule a matsayin kasa”, ya ce.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Aims for 500,000 Barrels Daily by July, eyes stock market debut

Also the chairman Aliko Dangote has equally announced intentions to list the refinery on the Nigerian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.