Home / News / Sakon Fatan Alheri Na Sabuwa SHEKARA Daga Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa

Sakon Fatan Alheri Na Sabuwa SHEKARA Daga Shugaban Jam’iyyar PDP Na Kasa

 

Yan Uwana Abokan Gwagwarmaya,

 

 

A dan lokaci kadan da ya gabata mu ka fara wata sabuwa tafiya ta shiga wannan sabuwa shekara ta 2022. Kamar irin shekara wadda ta gabata, kowanen mu nada buri na fata ga abin da yake da shi a zukatunsa, don samar da ingantaciyar rayuwa garemu da na iyalan mu.

 

 

Yana da muhimmanci gareku baki daya, yan uwana ku rayu tare da sanya fata nagari.
Tabbatar da gaskiya da adalci a matsayin muhimmin abin da ya tabbatar damu har tsawon wannan lokaci a cikin nasara da galaba ga fargaba da aka sanya mu, ba don haka ba, da kuwa mun shiga tasku da wahala, sabanin abin da ake ganin an canza tafiya ta mulki mai amfani ga al’umma.

Kada muyi saurin tunani ga cewar wannan Gwamnatin ta APC zata iya canzawa na wani tsarin tafiya a shekara 2022. Hakika zasu ci gaba da ganin sun kara sanya rayuwar mu a cikin matsi da wahala tare da barazana mai muni garemu.

 

Sai dai kyakyawan albishir shine; duk wahala tana da iyaka, irin wadanan matsalolin rayuwa da APC suka janyo mana zasu zama tarihi.

Sakamakon haka ina kara tunatar daku na ku fita kuyi rajista, ku tabbatar da kun mallaki katin zabe; fitowa don ganin mun yaki mugayen dabi’u a cikin rayuwa al’umma na daga cikin muhimmin kalubalen dake gabanmu baki daya.

Dangane da haka nake ganin shekara 2022 na da muhimmanci ga samun nasara da fatan alheri ga dukkan yan Nijeriya.

 

A madadin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP ina yiwa juna fatan shekara ta gari, shekara da zata samar da tabbatacen tsauni ga ceto al’umma, sake gina kasarmu Nijeriya bisa tubalin aminci da gaskiya da ci gaba.

Allah Ya taimake mu.

Dr. Iyorchia Ayu
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.