Home / Labarai / Samuel Aruwan Ya Kaddamar Da Katafaren Gini A Rundunar Sojan Sama Ta Kaduna

Samuel Aruwan Ya Kaddamar Da Katafaren Gini A Rundunar Sojan Sama Ta Kaduna

Kwamishinan kula da harkokin tsaron cikin gida da al’amuran cikin gidan na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya kaddamar da wani katafaren ginin da aka Sanya sunan marigayi ACM Christian Nkwuo a kadadin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i.
An dai yi wannan kaddamarwa ne jim.kadan bayan an kammala farin wadanda suka gama makarantar sojojin sama (BMTC) 40/2019, a matsugunnin sojojin sama da ke kaduna.
Hoton
A wannan hoton za a iya ganin su sanata Bala Ibn Na Allah da sauran wakilan yannmajalisa da suka halarci taron bude ginin da aka sanya wa suna wadansu Gwarzayen sojoji
ACM Nkwio, ACM Austine Atti da Mustapha Ibrahim sun rasa ransu ne a lokacin suna bakin aiki a Alkilubu, a karamar hukumar Kachiya da karamar hukumar Birnin Gwari a watan Janairu na  shekarar 2020. Allah ya gafarta masu.
Shugaban rundunar sojan saman Nijeriya Sadiq Baba ya tunawa wadanda aka dauka aikin sojan saman su 2,079 irin Jan aikin da ke gabansu saboda sun shiga aikin sojan ne a lokacin da ake samun matsalolin tsaron cikin gida kuma rundunar take gudanar da aiki kan jiki kan.
Samuel Aruwan ya kuma bayyana cikakkiyar godiya ga shugaban rundunar sojan saman Nijeriya Sadiq Baba Abubakar bisa irin kokarin da yake yi game da lamarin tsaron cikin Jihar Kaduna.
Aruwan ya ci gaba da cewa hakika wannan wata dama ce ta samun damar haduwa da shugaban Kwamitin sojojin sama na majalisar Dattawa Sanata Bala Ibn Na’ Allah, da wakilin shugaban kwamitinnkula da harkokin sojojin sama na majalisar wakilai Honarabul Tyough Aondona da kuma mataimakin shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai honarabul Makki Yalleman.

About andiya

Check Also

GWAMNA DAUDA LAWAL YA HARAMTA HAƘAR MA’DINAI BA BISA ƘA’IDA BA

…YA UMURCI JAMI’AN TSARO SU ƊAUKI TSATTSAURAN MATAKI Daga Imrana Abdullahi A yau Asabar, Gwamnan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.