Home / Lafiya / Samuel Aruwan Ya Kama Motocin Yan Badda Bami Shake Da Mutane A Kaduna

Samuel Aruwan Ya Kama Motocin Yan Badda Bami Shake Da Mutane A Kaduna

 Imrana Abdullahi
A kokarin da kwamishinan kula da tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan keyi domin dakile matsalar masu kwararowa cikin Jihar ta barauniyar hants inda ya samu nasarar Damke wata motar daukar kaya shake da mutane da aka saka su da nufin dole sai an shigar da su cikin Jihar kaduna
A wani samame domin tabbatar da ana bin dokar hana fita domin zama a gida da kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya kai wadansu wuraren da masu kunnen kashi suke an ga wadansu motoci da aka yi baddabamin cewa sun dauko kayan abinci ne amma mutane ne ake kokarin shigowa da su cikin kaduna.
Ita dai wannan motar da aka yi baddabamin da ake safarar mutane da ita an tare ta ne a ranar Litinin inda aka ba su umarnin su koma Jihar Kano wurin da suka fito, saboda an same su ne a kan ziyarar Jihar kano da kaduna.
Wannan lamari dai ya faru ne a kauyen Sabon Gida a karamar hukumar Ikara, da ke da kan iyaka da karamar hukumar Kiru a Jihar Kano.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a kan ziyarar Kano da Kaduna Kwamishinan kula da tsaro da  harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, cewa ya yi ” kamar yadda kuke gani, muna nan a kan ziyarar Jihar kaduna da Kano domin ganin irin yadda ake bayar da hadin kai da goyon baya game da dokar hana fita da zirga zirga a tsakaninmu musamman ga matafiya, sai gashi min samu nasarar kama wata babbar motar daukar kaya da ake safarar mutane da ita ana shigowa Jihar kaduna.
 
” kuma cikin hukuncin Allah mun samu nasarar kama mutane da yawa a cikin wannan motar da aka shirya su tsaf a cikinsa.

Aruwan, ya kara da cewa ” abin farin ciki shi me ba su kai ga shiga Jihar Kaduna ba kuma a yanzu mun mayar da su inda suka fito.

Mun kuma mayar da fasinjoji da yawa inda suka fito za kuma mu ci gaba da yin aikin domin ganin an kiyaye doka da ka’idar zirga zirga da Gwamnati ta Sanya, domin bin umarnin Gwamnati ne mafita.

“Hakika muna da matsalar wadanda ke gujewa shingayen jami’an tsaro suna Yankewa cikin daji musamman masu amfani da Baburan hawa amma zamu samu nasara a kansu nan bada komawa ba.

 Kwamishinan ya kuma samu nasarar zuwa kan ziyakar karamar hukumar Kudan da Danja a Jihar Katsina.

A lokacin da yake yi wa jami’an tsaro jawabi a kan ziyarar Jihar Katsina da Danja ya yi masu godiya ga jami’an tsaron a kan irin ayyukan da suke yi domin yaki da cutar Covid- 19, da ta addabi duniya baki daya.

 Sai da Kwamishinan tun da farko ya tarwatsa gungun Daruruwan yan kasuwa da suke cin kasuwa a kwantar Farakwai, a karamar hukumar Igabi a kan babbar  hanyar Kaduna zuwa Zariya.
An dai samu nasarar kama wadanda suka karya dokar a kan iyaka an kuma mikawa jami’an tsaro domin su fuskanci hukunci.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.