Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar ya kaddamar da rabon kayan abinci ga magidantan Talatar Mafara da ke cikin Jihar Zamfara.
Bayanan da muka samu ya tabbatar mana cewa kowane magidanta guda biyu an ba su kwali daya su raba da katon kwallin ya kunshi Taliya, Makaroni da Shinkafa”.
Bayan haka kuma ya dauki nauyin dalibai kowace karamar hukuma a fadin kananan hukumomi 14 na Jihar da za a zakulo mashi a kalla dalibai dari da Hamsin da zai dauki nauyin tallafin karatunsu a makarantun jami’a ko kwalejojin ilimi, kwalejin kimiyya da fasaha da kuma kwalejin horon malamai.
Wanda a halin yanzu dai ana ganin fagen siyasar Jihar Zamfara ya fara daukar sabon salo musamman ma na tafiya da daukacin al’umma baki daya.