Home / KUNGIYOYI / Sanata Kabiru Gaya Ya Tallafawa Masu Tallar Aiyukansa A Kafafen Labarai

Sanata Kabiru Gaya Ya Tallafawa Masu Tallar Aiyukansa A Kafafen Labarai

Imrana Abdullahi
A kokarin da Sanata Kabiru Gaya daga Jihar Kano ke kokarin karfafa Gwiwar masu yada ayyukansa a kafar Sada zumunta na zamani aka tallafa masu da kudi domin su samu saukin yin hidimar Sallah.
Ga dukkan wanda ya san Sanata Kabiru Gaya, ya san shi ne mutumin da ake kira mai gayya mai aiki da ke ayyukan ci gaban jama’a kamar wanda yake aiki da kasafin kudi
Aikace aikacen nasa a fili suke a bayyane da dukkan al’umma ke amfana.
Sanatan mai wakiltar yankin Kano ta Kudu ya karfafawa masu yi masa hidima ta fuskar goyon baya suna tallata ayyukan da ya yi wa jama’a ne da kudi ta yadda za su samu saukin yin hidindimun Sallah.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun Ma’aji Mai Nasibi, mai taimakawa Sanata Kaboru Gaya na musamman a kan harkokin kafafen yada labarai da babban hadimin Sanatan a kan harkokin yada labarai Kwamared Idris  ya aikewa da kafafen yada labarai.
Takardar dai ta ci gaba da bayanin cewa an yi taron mikawa jama’a kudin ne a wajen wani taron da aka yi a Jihar Kano.
Daukacin wadanda suka amfana da kuma yayan jam’iyyar APC sun nuna farin cikinsu da wannan tsarin bayar da tallafin da mai gayya mai aiki Sanata Kabiru Gaya, ya taimakawa mutanensa da ke aikin yada ayyukansa domin duniya ta shaida.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.