Home / Labarai / Kudancin Kaduna: Shugaban Yan Sanda Ya Bada Umarnin Aiki Da Doka

Kudancin Kaduna: Shugaban Yan Sanda Ya Bada Umarnin Aiki Da Doka

 Imrana Abdullahi
Shugaban yan sanda na kasar tarayyar Nijeriya ya yi kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaro baki daya domin ganin dokar hana fita da aka kafa ta yi tasiri.
A kokarin ganin an dawo da doka da oda a yankin Kudancin kaduna da a kwanan nan yake fama da matsalar Tashe tashen hankali da matsalar tsaro yasa shugaban yan sanda na kasa M. A Adamu, NPM, mni ya bayar da umarni ga kwamishinan yan sanda na Jihar Kaduna da ya tabbatar da bin doka da oda a game da dokar hana fitar da aka kafa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da mai magana da yawun rundunar yan sanda ta kasa DCP Frank Mba ya fitar inda aka rabawa manema labarai.
Kamar yadda takardar ta bayyana cewa an kafa wannan dokar hana fita ne domin kare lafiya da dukiyar jama’a
Kwamishinan yan sandan Jihar Kaduna ne da kansa zai jagoranci tsare tsaren aiwatar da dokar domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Jami’an tsaron da za su yi aikin bayar da tsaron sun hada da Yan Sanda, Sojoji da sauran jami’an kula da tsaro baki daya.
Shugaban rundunar Yan Sandan na kasa ya jajantawa al’ummar da wannan doka ta shafa musamman wadanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu sakamakon rikicin.
Ya ba su tabbacin cewa rundunar Yan Sandan za ta yi dukkan mai yuwuwa a iya karfinta a tsarin doka domin ganin an samu zaman lafiya a dukkan wuraren da lamarin ya shafa.
Shugaban Yan sandan na kasa ya yi kira ga jama’a da su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jami’an tsaron da za su yi wannan aikin. Ya kuma gargadi yan tayar  da hankali da su yi nesa da irin wannan mugun halin nasu na tayar da fitina.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.