Home / News / Sardaunan Badarawa Ya Kayar Da Mr LA, Da Kuri’a 210

Sardaunan Badarawa Ya Kayar Da Mr LA, Da Kuri’a 210

Usman Ibrahim wanda aka fi Sani da Sardaunan Badarwa ya zama dan takarar jam’iyyar PDP bayan sake zaben fitar da Gwani da aka yi a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba 2022.

 

Sardaunan Badarawa ya samu kuri’u 210 daga cikin yawan kuri’un da aka kafa 221 a lokacin zaben, wanda hakan ya bashi damar yi wa Mr LA kaye da ya samu yawan kuri’u biyar daga yawan mutanen da suka halarci zaben wato masu kada kuri’a ( deligetes) su 223 da aka tantance kafin fara zaben kuma sun fito ne daga kananan hukumomi Bakwai na mazabar dan majalisar Dattawan Kaduna ta tsakiya.

Kananan hukumomin sun hada da Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Igabi, Giwa, Birnin Gwari, Kajuru da Chikun.

Da yake sanar da sakamakon zaben shugaban Istifanus Caleb, ya ce kasancewar Usman Ibrahim Sardaunan Badarawa ya samu yawan kuri’un da ya fi na kowa ne dan takara, saboda haka ne ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe kuma shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a matakin zaben majalisar Dattawan shiyyar Kaduna ta tsakiya a shekarar 2023 mai zuwa.

Ya ce daga cikin masu zabe wato deliget 223 da aka tantance kuma ake saran su yi zaben, 221 sun kafa kuri’arsu kuma kuri’u hudu sun lalace.

Celeb ya kara da cewa Mr LA da Farfesa Usman Mohammed sun zo na biyu da na uku da kuri’u Biyar da kuda biyu.

Celeb ya bayyana zaben a matsayin wanda aka yi mai cike da adalci da tsare gaskiya da babu matuidi ko tursasa wani,ya Lara da cewa masu zaben da suka halarta duk kowa ya zabi abin da yake

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.