Home / News / ZA MU KAFA GWAMNATIN HADIN KAN KASA – MICHEAL AYUBA AUTA

ZA MU KAFA GWAMNATIN HADIN KAN KASA – MICHEAL AYUBA AUTA

…..Ta hanya ta Mutane Sama Da 300 Sun Samu Miliyoyin naira 
DAGA IMRANA ABDULLAHI
An kira ga dimbin matasan Najeriya da su tabbatar da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jam’iyyar Lebo ( Labour party) da za ta Ceci tarayyar Najeriya daga halin da take ciki.
Injiniya Micheal Ayuba Auta ne dan takarar neman kujerar majalisar Dattawa daga yankin Kudancin Kaduna ya yi wannan kiran a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron hadin kai tsakanin al’ummar Musulmai  da Kiristocin Jihar Kaduna wanda jam’iyyar Lebo ta shirya domin tattaunawa da kuma fadakar da Juna, da aka yi a makarantar St Anne’s da ke cikin garin Kaduna.
Injiniya Micheal Auta ya ci gaba da bayanin cewa kasancewar ko a kwanan nan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta tabbatar da cewa alkalumman da take da du sun tabbata cewa matasa a kalla miliyan Takwas ne daga cikin jerin wadanda suka yi rajistar Jefa kuri’a duk matasa ne kuma akwai kyakkyawan zaton cewa duk za su zabi jam’iyyar sa ta Lebo ne domin rayuwarsu ta inganta.
“A cikin kowace al’umma matasa ne kashin bayan ci gaban kasar a koda yaushe, misali kamar ni a Jihar Kaduna kuma a Unguwar Rimi inda na taso tun da aka haife ni, na san akwai dimbin matasan da ba su da aikin yi ko kadan, ga su nan da takardar gama makaranta amma ba abin yi sai Yawo kawai da takardun kammala makaranta kawai. A can baya masakun da muke da su su na gogayya da masakun da suke a Legas, amma a yanzu guda nawa ke aiki? kuma me ya faru da masakun da muke da su, ina batun babbar masana’anta kamfanin da ke Ajakuta, wanda kowa ya Sani kafin zuwan Gwamnatin APC sun ce mana za su kawo canji shin an samu canjin a nan bangaren, kuma ina batun jawo Teku a kawo Arewa shin an samu nasara? Shin me ya sa mu da ke Arewa idan za mu shigo da kayayyaki daga kasashen waje ta ruwa sai dai mu shigo da kaya ta ruwan Legas? Ina tashar Jirgin ruwa ta Lekwaja da du ka yi alkawari shin sun aiwatar? Sai kawai mu zauna muna ta kallo kawai.
“Jam’iyyar Lebo, wata tafiya ce da ake kokarin kawo gyara a kasa baki daya kuma lamarin ya fara a halin yanzu , ku duba dan takarar shugaban kasar mu ya tabbatar da samar da ayyukan ci gaban jama’a a duk inda ya samu kansa, Mu duba irin yadda kowane dan siyasa yake gudanar da harkar inganta rayuwar jama’a shin me kowa ya yi? Ku duba fa, a yau sama da shekara daya kwalejojin ilimi da kuma jami’o’in Najeriya duk su na rufe ba a karatu dalibai duk su na gida. To, sai a ce me kuma? Sai matasa kawai su rungume hannu
” Yanzu fa akwai matsala sosai ko a nan cikin garin Kaduna, a dhekarun baya can zaka iya zuwa kowace Unguwa ba tare da jin ko dar a zuciya ba, amma a yanzu saboda matsalar matasa kowa na tsoron yin tafiya daga wannan unguwa zuwa waccan domin akwai matasa a zube a kasa ba abin yi.
A game da batun takararsa ta dan majalisar Dattawa daga yankin Kudancin Kaduna, sai ya ce “Ni a iyakar Sani na babu jam’iyyar PDP  yankin Kudancin Kaduna, idan kuma mutum na maganar jam’iyyun APC da PDP ne a yankin Kudancin Kaduna duk na san su domin na yi masu aiki da karfina da kudi na Dukiya ta ta magantu a kansu dukkansu”.
A shekarar 2019 ni ne na kasance wanda ya bayar da tallafin da ya fi na kowa, na bayar da makudan kudi na ba su sun ci zabe, shin ina alkawarin da aka yi
Shin mutanen da suke yin wakilci daga bangaren Kudancin Kaduna me suka yi wa jama’ar yankin domin a samu ci gaba? shin a yankin Kudancin Kaduna me muke da shi?
“Kamfanin sarrafa Jinja da ke Kachiya, wanda marigayi Abdulkadir Balarabe Musa ya Gina lokacin mulkin Shagari, kamfanin Fulawa na Kafanchan tuni an Sanya shi a kasuwa, ku duba da duk da yan majalisar wakilai, Yan majalisar Jiha da Dattawa da muke da su shin me suka yi wa jama’a?
A cikin tarihi na a matsayin Injiniya Micheal Auta dan takarar majalisar Dattawa daga Kudancin Kaduna, ” Na yi sanadiyyar matasa da yawa sama da dari uku sun zama masu miliyoyin kudi, aje a bincika, na taimaka masu a bangaren ilimi, kuma ni ina cikin mutanen da suka Sanya hannun jarinsu mafi yawa domin samar da jami’ar NOK, mu uku muka hada kai domin samar da jami’ar, amma saboda bakin cikin abin da muka yi sai aka je da korafi a kan wani mutum daya daga cikin mu. Saboda haka da yardar Allah kudin mu na gaskiya ne ba cuta ko kadan a ciki, don haka ni Injiniya Micheal Ayuba Auta, za mu ci gaba da jami’ar in Allah ya amince ba wanda zai dauke jami’ar daga gare mu domin kawai akwai wata matsala a rare da dayan mu”.
“A bisa irin yadda lamuran ke tafiya a halin yanzu za a iya cewa jam’iyyar Lebo ce za ta kafa Gwamnatin Jihar Kaduna da Najeriya baki daya, saboda kowa na ji a jikinsa irin halin da ake ciki a duk fadin kasa baki daya.
Micheal Auta ya kara da bayanin cewa shi a matsayinsa na dan kasa nagari ya na kira ga al’umma da su hada kansu a kafa Gwamnatin hadin kan kasa.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.