Home / Ilimi / Sarkin Yaki Bello Kagara Ya Gina Cibiyar Koyar Da Na’ura Mai Kwakwalwa

Sarkin Yaki Bello Kagara Ya Gina Cibiyar Koyar Da Na’ura Mai Kwakwalwa

Sarkin Yaki Bello Kagara Ya Gina Cibiyar Koyar Da Na’ura Mai Kwakwalwa
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin ci gaba da ganin ya inganta rayuwar al’ummar birni da karkara Sarkin Yakin Danejin Katsina na farko Alhaji Bello Husaini Kagara a gina cibiyar Koyar da na’ura mai kwakwalwa a mahaifarsa da ke cikin garin Kagara a karamar hukumar Kafur Jihar Katsina arewacin tarayyar Nijeriya.
Ita dai wannan cibiyar tsohon shugaban hukumar bunkasa kanana da matsakaitan Masana’antu ta Nijeriya Alhaji Bature Umar Masari ya bude ta tare da dimbin jama’a da duka hada da Hakimin Mahuta Alhaji Bello Abdulkadir Yammama da sauran dimbin jama’a da dama.
Alhaji Bature Umar Masari ya yi kira ga daukacin jama’a baki daya da su yi ko yi da dan kishin kasa mai kokarin taimakawa al’umma Dare da rana safiya da maraice Alhaji Bello Kagara Sarkin Yakin Danejin Katsina na farko.
“Hakika muna alfahari da mutane irinsu Bello Kagara a cikin al’umma kuma sai ga shi Allah ya ba mu shi a cikinmu a Karamar hukumar Kafur cikin Jihar Katsina, muna yi wa Allah godiya da wannan kyautar da ya yi mana da mai kishin jama’a”.
An dai bayyana karatun na’ura mai kwakwalwa da cewa hanya ce da ke samar da ci gaban al’umma baki daya kasancewarta wani fage ne da ke bayar da damar samun dukkan wani ilimin da ake bukata.
“Idan an yi karatun na’ura mai kwakwalwa zai bayar da damar samun sana’a da mutum zai dogara da kansa, ga shi fage ne da ake samun dama kala kala daban daban”.
Kamar yadda wakilinmu ya ganewa idanunsa a cikin katafaren dakin da aka gina an ajiye sababbin komfutoci da aka bude a cikin Ledarsu da dukkan kayan da ake amfani da su a jikin na’ura mai kwakwalwa domin taimakawa daliban makarantar Firamaren garin Kagara da kewaye.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.