Home / Ilimi / Shaikh Dahiru Bauchi Ya Shawarci Al’ummar Musulmi Su Yi Rigakafin Korona

Shaikh Dahiru Bauchi Ya Shawarci Al’ummar Musulmi Su Yi Rigakafin Korona

Mustapha Imrana Abdullahi
Sanannen Malamin addinin musulunci, shaikh Dahiru Usaman Bauchi ya yi kira ga daukacin al’ummar musulmi da su rungumi allurar Rigakafin maganin cutar Korona domin samun ingantacciyar lafiya.
Malamin addinin musuluncin ya yi wannan kiran ne a gidansa lokacin wata ziyarar bude bakin da wata kungiyar yan jarida mai zaman kanta da ke yaki da cutar foliyo, (JAP).
 
Ya ce “Cutar Korona gadkiya ce, don haka tuni an yi Mani allurar Rigakafin na Korona saboda haka ne nake shawartar dukkan musulmi da su tabbatar an yi masu allurar domin muhimmancinta”.
 
 

Malamin ya bayyana Korona a matsayin wata annobar duniya da ke addabar kasashen duniya don haka lamarin ke bukatar taimakon kowa a cikin al’umma.

Shaikh Dahiru Usman Bauchi Bauchi shawarci daukacin musulmi su ci gaba da yin amfani da Takunkumin rufe baki da hanci da kuma wanke hannu a kai a kai tare da amfani da dukkan matakan da za su yi maganin annobar Korona da nufin tabbatar da matakan kariya.
 
 
Malamin addinin ya yi alkawarin taimakawa al’amuran yaki da cutar Korona a kowane mataki da nufin kawo karshen cutar a Nijeriya da duniya baki daya.
 
Shaikh Bauchi ya yi magana a kan cututtukan zazzabin lassa, bakon Dauro,Amai da gudana da kuma cutar murar tsuntsaye da dai sauransu ya na mai cewa jami’an kiwon lafiya da hukumomin lafiya ya dace su kara himma da nufin samun abin da ya dace.
 

Da yake gabatar da jawabi Kodinetan kungiyar yan jarida masu yaki da cutar foliyo a cikin al’umma, Alhaji Lawal Dogara godiya ya yi wa Malamin addinin shaikh Dahiru Usman Bauchi kasancewarsa a kan gaba wajen yada al’amuran lafiya a lokacin bayanansa da wa’azinsa don haka ya shawarci musulmi da su rungumi shawarar babban Malamin.

 

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.