Daga Imrana Abdullahi
Fitaccen Malamin addinin musulunci da duniya ta san da shi Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya gargadi shugaba Tinubu na Tarayyar Najeriya game da daukar matakin soji kan sabuwar gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wani malamin addinin Islama kuma shugaban darikar Tijjaniya a Najeriya ya yi wannan gargadin, ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar da kada ta amince da bukatar da shugaban Najeriya ya gabatar na kowane irin yaki da za a kaiwa jamhuriyar Nijar din.
Shaikh Dahiru Bauchi ya mashawarcin shugaba Tinubu da kungiyar kula tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a maimakon fada da Nijar ya kamata su tattauna da gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta hambarar da shugaba Mohammed Bazoum.
Ya bayyana hakan ne a Bauchi yayin da yake tattaunawa da ‘yan jarida, inda ya kara da cewa Najeriya da jamhuriyar Nijar na da dadadden zumuncin da ke bukatar karfafa shi domin a ci gaba da samun kwarin gwiwa.
“Yan Najeriya da Nijar sun hade. Don haka akwai bukatar gwamnatin tarayyar Najeriya ta shiga harkokin diflomasiyya da nufin karfafa kyakkyawar alakar bunkasar tattalin arziki da ci gaban kasashen yammacin Afirka biyu,” in ji Sheikh Dahiru.
A cewar Shehin Malamin, idan har Najeriya za ta shiga yaki da Nijar, da yawa ba kawai za su sha wahala ba, har ma za a kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, yana mai gargadin cewa, “yana da kyau a samar da wani kuduri na aminci don kaucewa zubar da jinin wadanda ba su ji ba ba su gani ba”.
Daga nan sai ya bukaci sauran shugabannin Afirka ta Yamma da sauran masu ruwa da tsaki da su rungumi harkokin diflomasiyya domin hakan zai taimaka a warware matsalar cikin ruwan sanyi.
“Muna kira ga Shugaba Tinubu muna kuma kira ga majalisar dokoki ta kasa da dukkan shugabannin kungiyar ECOWAS da masu ruwa da tsaki da kada su shiga cikin yaki a Nijar.
“Wannan shi ne don ceto rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da kuma ceto mutane daga fadawa cikin mawuyacin hali,” in ji Sheikh Bauchi.