Daga Imrana Abdullahi
Shugaban Kungiyar Masu Noman Zamani na kasa Honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri Dan marayan Zaki, da ke magana da yawun Manoma miliyan 25, ya yi kira ga shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu da ya gaggauta daukar mataki mai tsanani ga dukkan wasu yan fashin daji da suke yin barazana ga harkar Noma.
Aliyu Muhammad Waziri ya ce kasancewar Noma da samar da ingantacce kuma wadataccen abinci a kasa ne abin da ya fi komai muhimmanci saboda haka ne yake yin kira da a samu dokar ta baci ga harkar Noma.
Aliyu Waziri dan marayan Zaki ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin mu ya dandalin Sada zumunta na whattsapp.
Honarabul Aliyu Waziri ya ci gaba da bayanin cewa rashin samar da wadataccen abinci barazana ce a kasa don haka ya zama wajibi ga shugaban kasa ya tabbatar da Sanya dokar ta baci ga duk wani mai son haifarwa da lamarin Noma tarnaki musamman ga yan fashin daji da suke yi wa manoma da harkar Noma barazana a kasa Najeriya.
Waziri ya ce ” Domin harkar tsaro abu ne da ya ta’allaka a wuyan Gwannati, kasancewar abu na farko ya dukkan jami’an tsaro sun yi alkawarin cewa za su kare kasa daga kowace irin barazanar da za ta kawo cikas a kasa. Munsan jami’an tsaron suna kokari amma dai a kara kokari, domin ba hadarin da ya kai barazana wajen samar da abinci a kasa. Ina tabbatar wa da jama’a su Sani cewa yaki da matsalar rashin abinci ta fi yaki da makami ina tabbatar da hakan sai dai abin da za a iya hada shi da hakan sai dai batun lafiya”.
A bisa ga hakan ne “nake yin kira ga shugaban kasa da ya gaggauta daukar matakin katta kwana a harkar Noma don haka muke yin kira da lallai duk abin da za a yi a tabbatar da Sanya dokar ta baci a harkar Noma. Musamman yaki da yan fashin daji da harkar Noma a Najeriya domin rashin yin Noma a kasa ba zai haifar mana da da mai idanu ba domin karya tattalin arzikin kasa ne kawai”.
A kan haka ne nake yin kira ga dukkan wadanda abin ya shafa da su hanzarta daukar matakin gaggawa da fatan masu aikata wannan aikin na Ta’adda Allah ya shirye su mu kuma Allah ya kare mu.