Home / Labarai / Shugaban Jami’an Tsaron Farin Kaya Ta  “NSCDC” Dokta Audi Ya Karyata Batun Zargin Cin Hanci

Shugaban Jami’an Tsaron Farin Kaya Ta  “NSCDC” Dokta Audi Ya Karyata Batun Zargin Cin Hanci

Mustapha Imrana Abdullahi
 Babban Kwamanda Janar na rundunar tsaron farin kaya ta “NSCDC” Dokta Ahmed Audi a ranar Litinin a Abuja ya Karyata batun zargin cin hancin da ake dangantaka da shi da wasu ke yadawa a kafafen Sada zumunta na yanar Gizo.
Babban Kwamandan na NSCDC ya dai Karyata wannan batun cin hancin ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Daraktan bangaren yada labarai na hukumar Mista Olusola Odumosu, da aka rabawa manema labarai cewa “wani labarin da ake yadawa ya ja hankalin mahukuntan rundunar inda ake zargin shugaban rundunar Dokta Audi da batun cin hanci.
Saboda haka suke bayar da shawara tare da jan hankalin jama’a da ka da su amince da duk wani batun da zai karkatar da tunaninsu game da wani batun kanzon kurege da ake yadawa da zai bata mutunci da kuma neman karkatar da Dokta Audi game da aikin da ake aiwatarwa na ciyar da kasa gaba.
Kamar yadda ya ce, rundunar ba ta da wani nufin yin ja in ja da duk wata kafar yada labarai ta yanar Gizo da suke yada bayanan karya, amma su na yi masu gargadi su gujewa yin hakan.
Kamar yadda kaamansa suka bayyana “rundunar za ta ci gaba da yin kokarin ganin ta rike martaba da darajar da aka santa da shi da dukkan ayyukan da take aiwatarwa domin ciyar da kasa gaba, wanda hakan zai ba ta damar samar da aiwatar da aikin da aka santa da shi”, inji Odumosu.
“Don haka rundunar ba ta da nufin yin ja- in- ja da kowa game da wannan batun cin hanci da ake yadawa, saboda haka babban Kwamanda tare da hukumar gudanarwar rundunar suke ba jama’a tabbacin cewa za su ci gaba da aiwatar da aiki bisa gaskiya da rikon amana”, inji shi.
“Aiwatar da aiki bisa gaskiya da rikon Amana da kuma kara Dora rundunar a kan dai- dai kamar yadda tsari da tanaje tanajen ma’aikatar da suke karkashinta suka tanadar”, inji shi.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.