Home / Labarai / Barnar Da Obasanjo Ya Yi Wa Arewacin Najeriya Sai An Shekara 100 Ba A Gyara Ba – Mahadi

Barnar Da Obasanjo Ya Yi Wa Arewacin Najeriya Sai An Shekara 100 Ba A Gyara Ba – Mahadi

Mustapha Imrana Abdullahi
Wani Fitaccen dan kasuwa kuma mai fafutukar kare hakkin jama’a dan asalin Jihar Katsina mazaunin Kaduna Dokta Mahadi Shehu, shugaban kamfanin rukunin kamfanonin Dialque, ya bayyana irin Barnar da Obasanjo ya yi wa yankin arewacin Najeriya da cewa sai yan arewa sun yi shekaru Dari (100) ba su gyara Barnar ba.
Dokta Mahadi Shehu ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da kafar Talbijin ta DITV a cikin shirin Ga Fili Ga Doki inda ya yi magana a kan makomar Arewa.
Mahadi Shehu ya ce idan ba wanda ya samu alamun tabin,hankali ko tsananin son zuciya ba ta yaya za a ce kawai wani ya mike tsaye kawai ya rika cewa a dauki mulkin da ya ragowa yan Arewa ku bani haka kawai.
Dokta Mahadi Shehu ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin mutanen arewacin Najeriya da zai iya magance irin Barnar da tsohon shugaba Obasanjo ya yi wa yankin arewacin Najeriya koda mutum zai shekara dari ne domin Barnar ta yi yawa kwarai.
Ya ci gaba da bayanin cewa a batun harkokin kasuwanci,Noma,Masana’antu,Wutar lantarki da dukkan fannoni duk sai da Obasanjo ya tabbatar ya mayar da yankin Arewa baya, wanda a halin yanzu muke fama da matsalar kuma ba mai iya warware ta cikin karamin lokaci.
Saboda haka nake fadakar da jama’a cewa idan aka sake aka mikawa wasu mulki ta hanyar tursasawa to, duk wanda bashi da gida a Nijar ya hanzarta zuwa ya saya domin dole sai an raba mu da kasar baki daya saboda kowa ya san an dauko hanyar yin hakan
“Ta yaya wani haka kawai zai ta shi ya rika tsammanin wai sai dole an bashi mulkin kasa a tsari irin na Dimokuradiyya? Ai ya dace ne kawai a samu tsarin irin na dai- daito a tsakanin yankin Arewa da duk wani da ba yankin yake ba idan ma har za a ba su mulki,amma ba da karfin tuwo ba idan kuma hakan ta faru to hakika mun gama yawo domin daba wa za a yi kawai a inda Obasanjo ya tsaya na mayar da yankin Arewa baya”, inji Mahadi Shehu.
Da yake magana a game da yan majalisun tarayya, Dattawa da suka fito daga yankin Arewa kuwa ya kara jaddada cewa su ba su ga wani amfaninsu ba sam domin har yanzu ba su tabbatar da wakilcin da ya dace ba.
“Daga cikin iftila’i Goma da yake fadawa kasar nan Takwas daga ciki a yankin Arewa ya fada duk kuma wannan na faruwa ne sakamakon irin sakacin da ake da shi a yankin, a duba a bangaren rasa rayukan jama’a,lalacewar lantarki,durkushewar masana’antu,an hana yan Arewa su yi Noma,Kiwon Dabbobi da durkushewar harkokin kasuwanci da muhimman al’amuran inganta rayuwa duk na Arewa ya fi ko’ina lalacewa a duk fadin Najeriya, kuma wannan duk sakaci ne ya kawo hakan”, inji Mahadi Shehu.
Mahadi Shehu ya kuma fadakar da jama’a cewa su tuna da a ina ne a Kudancin Nakeriya aka samu kauye ko wani Garin da aka kashe mutane 100 ko sama da hakan a rana daya?
Ya ce ko a kwanan nan an yi hakan a garin Gworonyo da ke cikin karamar hukumar Gworonyo a Jihar Sakkawato, akwai ma wurin da aka kashe mutane 170 a rana daya, don haka za a iya cewa idan aka yi duba sosai da idanun basira daga shekarar 1999 zuwa yanzu da Dawowar Dimokuradiyya ba abin da ya kawo wa yankin Arewa sai masifu iri – iri daban daban, wanda hakan ba ci gaba ba ne ga yankin Arewa.
“Amma sabanin wadansu wurare da kasashe idan kaje zaka yi sha’awar Dikokuradiyya misali a kasar Ruwanda da ka je zaka yi sha’awar Dimokuradiyya kwarai.
“A kasar Ruwanda fa Yakin basasa aka yi aka kashe mutum miliyan daya, aka wargaza kasar amma a yanzu halin da suke ciki babu wani abu mai kama da hakan sam komai ya koma dai- dai a kowane kauye akwai asibiti, kowane yaro na zuwa makaranta
Kuma Mutanensu sakamakon Yakin da aka kashe mutum miliyan daya kuma mutum miliyan hudu suka fice daga kasar a halin yanzu duk sun koma gida sai yan kalilan kawai da suke a waje wasu kasashe, ha makarantu nan ko’ina, shugabansu na kokarin yi masu adalci ba zaka ga wani gida na shugaban ba ban da inda yake ciki mai dakuna uku, idan kaga motarsa da yake amfani da ita sai ka yi ta dariya.
“Turawa da zuwa Riwanda yawon bude idanu, labarawa na zuwa Ruwanda, to me yasa ba a zuwa Najeriya domin mu Dimokuradiyyarmu ba irin waccan bace”.
“Saboda Dawowar Dimokuradiyya ya kara raba kawunan yan kasar nan, domin Dimokuradiyya ce a baki kawai, misali a fili kaga fuskar Annabi Musa amma a ciki can ta fir’auna ce haka lamarin yake

About andiya

Check Also

An Rantsar Da Ishaya Idi Sabon Shugaban Kasuwar Duniya Ta Kaduna

  Daga Imrana Abdullahi A kokarin ganin al’amura sun ci gaba da tafiya kamar yadda …

Leave a Reply

Your email address will not be published.