Home / Labarai / Shugaban Karamar hukumar Bakori Ya Jinjinawa Dikko Radda

Shugaban Karamar hukumar Bakori Ya Jinjinawa Dikko Radda

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban karamar hukumar Bakori da ke cikin Jihar Katsina Alhaji Ali Mamman Mai Citta, ya bayyana nadin da aka yi wa tsohon dan jarida ya shugabanci gidan rediyon Jihar Katsina da cewa an yi abin da ya dace a lokacin da ya dace domin a Sanya kwarya a cikin gurbinta.

Ali Mai Citta ya ce nadin Lawal Attahiru Bakori a matsayin Janar Manajan gudan rediyon Jihar Katsina abu ne da ya dace bisa cancartarsa

Alhaji Mamman Mai Citta, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci wata tawagar al’ummar mutanen Bakori da suka hada da Kansiloli da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa daga karamar hukumar inda suka je domin taya Janar Manajan gidan rediyon Jihar Katsina murnar nadin da Gwamna Dikko Radda ya yi masa.

Ya ce hakika nadin Lawal Attahiru Bakori zai taimaka kwarai wajen tafiyar da gidan rediyon ya aiwatar da aiki kamar yadda ya dace domin za a samu ingantattun shirye shiryen da suka dace

Alhaji Ali Mamman Mai Citta ya kuma bayar da shawara ga Janar manajan da ya yi amfani da kwarewarsa domin karfafawa Gwamna da Gwamnatin Jihar Katsina tare da al’umma Gwiwar a game da aikin da aka nada shi, wanda yin hakan zai taimakawa jama’ar karamar hukumar Bakori.

 

 

Shugaban karamar hukumar ya kuma yi godiya ga Gwamnan Jihar katsina Dikko Radda musamman game da yadda ya zabi yayan karamar hukumar gida biyu domin su jagoranci bangaren Noma da kuma harkar yada labarai, wannan abin godiya ne kwarai.

 

 

Da suke gabatar da jawabi biyu daga cikin masu ruwa da tsaki Alhaji Kabir Mamman da Alhaji Sanusi Magayaki cewa suka yi ana fatan Janar Manajan zai yi amfani da dimbin kwarewarsa wajen tafiya da kowa.

A nasa jawabin shugaban majalisar Kansilolin karamar hukumar Bakori Alhaji Muhammed Haruna jiniinawa Gwamnan Jihar Katsina ya yi musamman a game da yadda yake kokarin yin maganin matsalar tsaro, kamar yadda ya ce lamarin ya fara haifar da nasarar da ake bukata.

 

Da yake mayar da jawabi, sabon Janar manajan na rediyon Jihar katsina Alhaji Lawal Attahiru Bakori godiya ya yi ga mutanen karamar hukumar Bakori da suka kawo masa ziyara, inda ya tabbatar masu cewa zai ba marada kunya.

Alhaji Lawal Attahiru Bakori ya ce a dan kankanin lokacin da ya karbi ragamar tafiyar da gidan rediyon al’amura sun inganta kwarai ba kamar da ba

 

 

Sai ya shawarci masu ziyarar da a koda yaushe su kasance masu bayar da shawarwari na gari domin yadda za a ci gaba da samun ingantawar al’amura a Jihar da kasa baki daya.

 

 

Janaral Manajan ya bayar da tabbacin cewa zai rika mayar da hankhankali ga jama’a ta hanyar sauraren kowa a koda yaushe kasancewar kofarsa a bude take.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.